Dama na sha alwashin kai ka kasa, Asari Dokubo yayi martani kan kamen Nnamdi Kanu
- Asari Dokubo, tsohon kwamandan tsageru ya yi murna tare da cewa dama ya sha alwashin ganin bayan Nnamdi Kanu
- Dokubo ya sanar da yadda Nnamdi Kanu ya kallafawa 'yan Biafra biyan haraji duk shekara ko kuma a hana su shiga Biafra
- Dokubo ya zargi Kanu da zama babban dan damfara wanda ke wawurar kudaden Biafra kuma yana waddaka
Mujahid Asari Dokubo, tsohon kwamandan tsageru kuma shugaban gwamnatin gargajiya ta Biafra, yayi martani bayan sake kama Nnamdi Kanu, shugaban IPOB da gwamnatin tarayya ta yi.
Kanu, wanda ke fuskantar tuhuma kan cin amanar kasa, ya tsallake beli bayan wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta sake shi saboda matsalar lafiya, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Zulum zai sake gina garin Malam-Fatori bayan barinsa da aka yi na shekaru 7
KU KARANTA: Boko Haram: Sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda sanye da kayan sojoji a Borno
Bayan an bada belinsa, ya tsere zuwa Ingila
Ya tsere zuwa Ingila inda ya dinga bada umarni ga mambobin IPOB na kudu maso gabas a kan tada hazo a yankin. An sake kama shi a kasar waje kuma an dawo da shi Najeriya a ranakun karshen makon da ya gabata.
Makonni kafin kamensa, Asari Dokubo, wanda ya samu matsala da Kanu, ya sha alwashin lalata "shaidaniyar daular" Kanu.
"Nnamdi Kanu, bana cikin rukuninka, amma a wannan, sai na ga bayanka. Zan lalata daular dake aiki domin hanamu samun Biafra. Biafra yanzu kasuwanci ka mayar da ita, baka da wata hanyar samu sai ita. Abun takaici ne yadda jama'ar Ibo suka fada maka, amma lokacin ka yayi kuma zan kai gareka," Dokubo yace a wancan lokacin.
Mujahid Asari Dokubo yayi murnar kama Kanu
Bayan kwanaki da kama Kanu, Dokubo ya zundi shugaban IPOB inda yace yanzu ya fara shiga tsaka mai wuya.
A wani bidiyo, Dokubo ya zargi Kanu da damfarar 'yan Biafra inda yace har yanzu ya kasa basu kididdigar kudin da ake cirewa.
"Nnamdi Kanu, kamar yadda nayi alkawari, sai na kai ka kasa. Yanzu haukar ka ta fara, yanzu somin tabi ne. Ka cutar da 'yan Biafra kuma ka dinga kasuwanci da mu.
“Ka karba kudinmu da sunan kudin tsaro amma ka kasa bada bayani kan su. Kana son 'yan Biafra su dinga biyan kudi duk wata ko kuma ba za a bar su shiga Biafra ba. Ko a nan ai ka bayyana matsayin dan damfara.
“Ka ce ka bani N20 miliyan, bidiyo baya karya. A lokacin da na fara a shekarar da ta wuce, baka yi martani ba. Ka tura mabiyanka da su yi min martani kuma sun fadi abubuwa daban-daban.
"Ban taba zama dan IPOB ba, ka bani miliyan 20, fada mana, ta banki ne ko hannu da hannu. Ka kawo shaida."
Dokubo ya caccaki Kanu inda yace an tsare shi sama da sau saba'in amma bai bar kasar ba, SaharaReporters ta ruwaito.
A wani labari na daban, a kalla mutum bakwai aka kashe yayin da aka sace wasu goma a mabanbantan hare-hare da 'yan bindiga suka kai kananan hukumomin Chikun , Kajuru da Giwa a jihar Kaduna.
Daga cikin jama'ar akwai wasu hudu da aka sace tare da harbewa a yankin Tsohon Gayan dake karamar hukumar Chikun ta jihar yayin da wasu biyu aka kashesu a tashar Iri dake karamar hukumar Kajuru.
Moses Matthew, wani mazaunin tashar Iri dake karamar hukumar Kajuru ta jihar, ya sanar da ChannelsTv cewa 'yan bindiga sun dira yankin wurin karfe 1 na dare dauke da miyagun makamai kuma sun fara harbe-harbe.
Asali: Legit.ng