Ba zan yi murabus daga siyasa ba har sai na mutu, Malam Shekarau

Ba zan yi murabus daga siyasa ba har sai na mutu, Malam Shekarau

  • Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Ibrahim Shekarau yace ba zai yi murabus daga siyasa ba sai ya mutu
  • Shekarau yace siyasarshi ita ce addinin shi kuma addinin shi ita ce siyasar shi, don haka ba zai iya barin addini ba
  • Kamar yadda ya sanar, koda ba zai iya takara ba ya tsufa, zai zauna a gidansa yana bada shawarwari kan siyasa

Kano

Sanata Ibrahim Shekarau ya ce ba zai yi murabus daga siyasa ba har sai ya mutu, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan rantsar da majalisar Shura ta jihar Kano, Shekarau ya ce "ba ni da lokacin yin murabus daga siyasa har sai na mutu."

Tsohon gwamnan har sau biyu na jihar Kano, ya samu mukamin ministan ilimi daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kuma yayi fafutuka a zaben 2015 ba kadan ba.

KU KARANTA: Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda

Ba zan yi murabus daga siyasa ba har sai mutu, Malam Shekarau
Ba zan yi murabus daga siyasa ba har sai mutu, Malam Shekarau. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, a halin yanzu shi ke wakiltar mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.

Siyasata ita ce addinina, addinina shine siyasata

"A takaice, abinda yasa na zo ina magana shine in musanta lamarin. A wurina gaskiya babu ranar murabus daga siyasa.

“Ina fadin wannan kusan shekaru 20 da suka gabata. Siyasata ita ce addinina, addinina shine siyasata kuma babu lokacin da zan bar addinina saboda dukkan biyun suna aiki tare ne.

“Addini shine bautawa Ubangiji kuma kololuwar bautawa Ubangiji shine bautawa jama'a da suka kasance halittar Ubangiji. Kamar yadda na sani Musulunci ya koyar da cewa duk wani taimako da ka baiwa wani, kana cika umarnin Ubangiji ne. Idan na yi maka addu'a ko kyautatawa, nau'in ibada ne."

Koda na tsufa zan cigaba da siyasa

"Idan na kai shekaru 90 na tsufa ba zan iya takara ko fita gangamin siyasa ba, zan iya bada shawara ga jama'a ina daga kwance. Siyasa hanya ce ta bautawa jama'a, hakan na dauka.

“A don haka ne yasa nake tausayin duk wanda yace zai yi murabus daga siyasa. Ta yuwu bai gane mene ne siyasa ba. Sun tsayar da ita a samun mukami, fita takarar gwamna, sanata ko wani mukami.

“A fahimta ta, siyasa ita ce kwarewar mutum wurin mu'amala da jama'a tare da bautawa jama'a ta duk hanyar da ta kama. Don haka bani da ranar murabus daga siyasa. Ina nan har sai na mutu."

KU KARANTA: Zulum zai sake gina garin Malam-Fatori bayan barinsa da aka yi na shekaru 7

A wani labari na daban, mayakan ISWAP wadanda ba a san yawansu ba sun sheka lahira bayan arangamar da suka yi da jami'an tsaron hadin guiwa a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno.

'Yan ta'addan wadanda aka gani cikin kayan sojoji sun kai farmaki tare da budewa wata tawagar jami'an 'yan sanda wuta a yammacin Juma'a yayin da suke dawowa daga Buni Yadi kusa da Auno-Garin Kuturu a karamar hukumar Kaga.

An gano cewa 'yan ta'addan sun kwace wata mota daya da take mallakin jami'an tsaron, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng