Hotuna da bidiyon tsalelliyar Shuwa Arab da mataimakin gwamnan Neja yayi wuff da ita

Hotuna da bidiyon tsalelliyar Shuwa Arab da mataimakin gwamnan Neja yayi wuff da ita

  • Ahmed Muhammad Ketso, mataimakin gwamnan jihar Niger ya auri kyakyawar amarya Shuwa Arab
  • An yi kasaitaccen bikin inda amarya ta sha ado da kwalliya irin na al’ada
  • Hakan na zuwa bayan Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan shima ya auri tashi amaryar ‘yar Shuwa

Mataimakin gwamnan jihar Niger, Ahmed Muhammed Ketso ya auri tsalelliyar amarya ‘yar Shuwa Arab.

Shafin Instagram na northernblog_ ya wallafa bidiyon bikin inda aka nuno amarya da kawayenta cikin annashuwa da walwala.

KU KARANTA KUMA: Saƙo ga gwamnonin Kudu: Dole ɗan ƙabilar Igbo ne zai zama shugaban ƙasa, cewar Ohanaeze

Hotuna da bidiyon tsalelliyar Shuwa Arab da mataimakin gwamnan Neja yayi wuff da ita
Mataimakin gwamnan Neja, Ahmed Ketso da amaryarsa Hoto: hausaloaded.com
Asali: UGC

Amaryar tayi ado na gani na fada cikin shiga ta al’adar Shuwa yayinda shi kuma ango ya sanya farar shadda dinkin babban riga wanda ya sha aiki.

A cikin bidiyon, an nuna ango yana bude mayafin da amarya ta yi amfani dashi wajen rufe fuskarta, sannan ya sumbace ta a goshi kuma nan take sai wajen ya kaure da guda.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa a 2023: Tana shirin karewa Atiku, Kwankwaso, Tambuwal da sauransu

Mabiya shafin sadarwa sun yi martani a kan bikin

Wasu 'yan Najeriya da ke bin shafin sun tofa albarkacin bakunansu a kan bikin.

deedah_pastries_ng ta ce:

"Sadakallahul azeem,Alfatiha,to Allah ya basu zaman lafiya."

ag_boii ya ce:

"Har yanz daliban makarantar Islamiyya na tsare a hannun 'yan bindiga, tuni ne kawai."

roselinetasha ta ce:

"Matan Shuwa arab ake yayi yanzu. Lashe money kenan"

mustapha_s_idrees ya yi martani:

"Wai shuwa arab tab ai wlh gara nasamu tsaleliyar budurwa bahaushiya chocolate colour na aureta,kowa yabar gida,gida yabarshi."

Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da Zukekiyar Shuwa Arab

Hakan na zuwa ne bayan Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan yayi sabuwar amarya a sirrance a wani biki da ba a tara jama'a ba a jihar Borno.

SaharaReporters ta tattaro cewa sunan amaryar shugaban majalisar dattawan Zainab Algoni Abdulwahid, matashiyar budurwar Shuwa Arab.

SaharaReporters ta ruwaito cewa an yi bikin ne a sirrance domin gujewar cece-kucen jama'a yayin da amarya Zainab za ta koma Abuja a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel