Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita

Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita

  • Ahmad Ibrahim Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya auri kyakyawar amarya Shuwa Arab mai suna Zainab Algoni Abdulwahid
  • An yi bikin a sirrance ba tare da gagarumin taro ba a ranar Juma'a domin gujewa cece-kucen jama'a
  • Zukekiyar amarya Zainab za ta koma Abuja daga Maiduguri a ranar Lahadi kamar yadda majiya mai karfi ta sanar

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan yayi sabuwar amarya a sirrance a wani biki da ba a tara jama'a ba a jihar Borno.

SaharaReporters ta tattaro cewa sunan amaryar shugaban majalisar dattawan Zainab Algoni Abdulwahid, matashiyar budurwar Shuwa Arab.

KU KARANTA: Ganduje na kokarin tsige Rimingado saboda bincikar iyalansa da yake kan wasu kwangiloli

Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita
Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita. Hoto daga saharareporters.com
Asali: UGC

SaharaReporters ta ruwaito cewa an yi bikin ne a sirrance domin gujewar cece-kucen jama'a yayin da amarya Zainab za ta koma Abuja a ranar Lahadi.

Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita
Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita. Hoto daga saharareporters.com
Asali: UGC

Wani kwarya-kwaryan walima aka yi a gidan amaryar dake lamba 1, Gwange, layin Malut Shuwa dake Maiduguri.

"Shugaban majalisar dattawan Najeriya ya auri matashiyar budurwar Shuwa Arab a Maiduguri. Sunanta Zainab Algoni Abdulwahid.

"An daura musu auren ne bayan sallar Juma'a a Maiduguri. Amaryar zata kama hanyar Abuja zuwa ranar Lahadi.

"An yi bikin a sirrance ne. Shugaban majalisar dattawan bai halarci daurin auren ba amma ya tura wakilai kuma sun je har an daura.

Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita
Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita. Hoto daga saharareporters.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Kwamandojin Boko Haram da ISWAP na taro, NAF sun yi luguden wuta a yankin tafkin Chadi

"Amma amaryar tayi shagalin bikinta a gidansu dake Gwange, titin Malut Shuwa dake Maiduguri," majiyar ta sanar da SaharaReporters.

A yayin da aka tuntubi Ola Awoniyi, mai bada shawara na musamman ga shugaban majalisar dattawan kan yada labarai, ya ce yana filin sauka da tashin jiragen sama.

Bayan an tura masa sakon kar ta kwana, bai yi martani a kai ba.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta bada umarnin kama wani dan sanda a kan zarginsa da ake da karbar kudi hannun mutane tare da bukatar kwanciya da wadanda ake zargi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Akwa Ibom, Odiko Macdon, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar ga manema labarai a Uyo ranar Lahadi.

Macdon, dan sanda mai mukamin SP ya ce wannan abun da dan sanda yake yi an gano ne bayan wani Zion Umoh ya nadi bidiyon yayin da dan sandan mai suna Daniel Edet ke bukatar lalata da kuma karbar N60,000 daga wacce ake zargi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel