Kungiyoyin CAN da HURIWA sun buƙaci El-Rufai ya yi murabus bayan garkuwa da ɗalibai 26 a Kaduna

Kungiyoyin CAN da HURIWA sun buƙaci El-Rufai ya yi murabus bayan garkuwa da ɗalibai 26 a Kaduna

  • Kungiyoyin CAN da HURIWA sun bukaci El-Rufai ya bar kujerar sa saboda karuwar rashin tsaro a Kaduna
  • Shugaban HURIWA na kasa ya zargi gwamnatin tarayya da lallaba yan bindigar da suka addabi Arewa
  • Kiran na kungiyoyin na zuwa ne biyo bayan sace dalibai a makarantar Bathel Baptist School da ke Maraban Rido a Kaduna

Kungiyar kiristocin Nigeria (CAN) da kuma kungiyar marubutan kare hakkin dan Adam (HURIWA) sunyi kira ga gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya sauka daga kujerarsa ta gwamna saboda ta'azzarar matsalar rashin tsaro a jihar.

Kiran na su ya biyo bayan yadda gwamnan ya gaza a matsayinsa na shugaban hukumomin tsaro a jihar da kuma kin yin sulhu da yan garkuwa, The Guardian ta ruwaito.

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An kama wasu sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' a wata Coci a Abuja

Jiya, dalibai 26 yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar Bethel Baptist, Maraban Rido, Karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

Da take tabbatar da faruwar lamarin jiya, rundunar yan sandan jihar ta ce jami'an tsaro suna bibiyar yan bindigar.

Kungiyoyin HURIWA da CAN sun ce El-Rufai ya gaza

Shugaban CAN, reshen Kaduna, Rev. Joseph Hayab, wanda babban malamin cocin Baptist ne, yayi bayanin cewa daliban dake zaune a dakunan kwana kafin ayi garkuwar 180 ne, ya kara da cewa: 'mun kirga su da safiyar nan (Litinin) kuma ba a ga mutum 174 ba.'

Ya bukaci gwamnan da yayi murabus, idan ba zai iya magance matsalar tsaro a jihar ba. Amma El-Rufai ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma hadari ga al'umma kamar yadda rahoton na Guardian ya ce.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Daƙile Harin 'Yan Bindiga a Makarantar Fasto Oyedepo a Kaduna

Da take zargin El-Rufai da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan garkuwa da dalibai a Kaduna da sauran jihohin Arewa, HURIWA ta bayyana rashin kwarewar jami'an tsaro wajen kawo karshen matsalar.

A wata sanarwa da ya fitar jiya, shugaban HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya zargi gwamnatin tarayya da lallaba yan bindigar, ya kuma zargi El-Rufai da bawa yan bindigar dama ta hanyar sanya dan sa a makarantar gwamnati tare da cire shi a sirrance daga baya.

"Idan El-Rufai zai ci gaba da abin kunya ya kamata yayi murabus saboda ya cire dansa daga makaranta kuma yana ikirarin cewa yan bindiga na neman rayuwarsa. Sai gashi bayan awa 24, wadannan yan bindigar sun sace yayan talakawa da dama", a cewar HURIWA.

El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna

A wani labarin daban, gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin rufe wasu makarantu 13 nan take a wurare daban-daban a jihar, The Cable ta ruwaito.

Shugaban sashin kula da ingancin kayayyaki na ma'aikatar ilimi na jihar Kaduna, Umma Ahmed ce ta fitar da sanarwa.

An aike da sanarwar da shugabannin makarantu masu zaman kansu da abin ya shafa, sakon na mai cewa nan take za su rufe makarantun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel