Yanzu-Yanzu: El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna

Yanzu-Yanzu: El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna

  • Mutanen jihar Kaduna musamman dalibai na mkarantun frimare da sakandare na cikin mawuyacin hali
  • Rashin tsaro musamman a jihar da ke arewa maso yamma na barazanar kawo cikas ga tsarin karatun daliban
  • Dominkare afkuwar hare-haren a gaba kan dalibai, gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakin rufe wasu makarantu a jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin rufe wasu makarantu 13 nan take a wurare daban-daban a jihar, The Cable ta ruwaito.

Shugaban sashin kula da ingancin kayayyaki na ma'aikatar ilimi na jihar Kaduna, Umma Ahmed ce ta fitar da sanarwa.

Sace dalibai da aka yi a baya-bayan nan ya janyo zanga-zanga a Kaduna.
Sace dalibai da aka yi a baya-bayan nan ya janyo zanga-zanga a Kaduna. Kehinde Gbenga/AFP
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar jihar Kano ta dakatar da Muhyi Magaji

An aike da sanarwar da shugabannin makarantu masu zaman kansu da abin ya shafa, sakon na mai cewa nan take za su rufe makarantun.

Ta kuma yi gargadin hukuncin da ka iya biyo baya idan ba a bi umurnin ba.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Ana shawartar cewa a bi dukkan umurnin da ke cikin wannan wasikar domin akwai hukunci da zai biyo baya ga makarantun da ba su bi umurnin ba."

Ahmed ta ce matakin ya zama dole ne bayan dace dalibai da aka yi daga Bethel Baptist High School a Damishi da ke karamar hukumar Chikun.

Fiye da dalibai 100 ne aka nema aka rasa bayan harin da ake zargin yan bindiga ne suka kai a safiyar ranar Litinin.

Sai dai rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce an ceto dalibai 26 cikin wadanda aka sace.

Sanarwar ta ce:

"Bayan rahoton da hukuma ta samu game da barzanar tsaro a Bethel Baptist High School a Damishi, an yi taro da kungiyar masu makarantu masu zaman kansu (NAPPS) da wasu masu ruwa da tsaki a ranar Litinin 5 ga watan Yulin 2021 inda aka yanke hukuncin rufe wadannan makarantun daga ranar Litinin 5 ga watan Yulin 2021."

Makarantun da abin ya shafa

Makarantun sune Faith Academy da ke Kachia Road da ke kallon Jakaranda; Deeper Life Academy, Maraban Rido; Ecwa Secondary school, Ungwar Maje, Bethel Baptist High School, Damishi, da St. Peters Minor Seminary, Katari.

Saura su hada da Prelude Secondary School, Kujama; Ibiso Secondary School, Tashar lche; Tulip International (Boys) School; Tulip international (Girls) School; Goodnews Secondary School; St Augustine, Kujame; Comprehensive Development institution (CDI), Tudun Mare da Adventist College, Kujama.

KU KARANTA: Da Duminsa: Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Makarantar Fasto Oyedepo a Kaduna

Shugaban daya daga cikin makarantun da abin ya shafa, ta ce bata da masaniya kan taron da aka dauki wannan matakin.

"Na ga sakon ne kawai amma ba zan iya cewa komai a kai ba. Ba su kira mu taro ba. Kawai mun ga sakon ne. Ba su kira kowa wani taro ba," shugaban makarantar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa The Cable.

'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari

A wani labarin, yan bindiga sun sace mata 13 a tsakanin garuruwan Manini da Udawa da ke kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, a hanyarsu ta zuwa bikin daurin aure, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis misalin karfe 12 na rana a lokacin da yan bindigan suka tare motocci uku da ke dauke da matan a hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

An gano cewa cikin wadanda aka sace din akwai mata masu shayarwa da wata mata da yayanta mata biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel