An kama wasu sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' a wata Coci a Abuja

An kama wasu sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' a wata Coci a Abuja

  • An kama matasa biyar sanya da rigar #BuhariMustGo da suka yi yinkurin haddasa zanga zanga a wata coci a Abuja
  • An fita da matasan su biyar a motar hukumar DSS bayan da jami'an tsaron cocin suka mika su hannun hukumar kamar yadda Sowore bayyana
  • Wani jami'in cocin yace dole ne su kama matasan saboda basu san meye shirin su ba, yayin da Sowore ke kallon hakan a matsayin abun kunya

Wasu masu zanga zanga da suka sanya riga dauke da rubutun 'Buhari-must-go' don zuwa Cocin Dunamis Gospel mai hedikwata Lugbe, Abuja, sun shiga hannu kuma rahotanni sun ce tuni aka mika su ga rundunar tsaro ta farin kaya DSS, News Wire ta ruwaito.

Pastor Paul Eneche
Pastor Paul Eneche. Hoto: News Wire
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: El-Rufai: Dalilan da yasa bai zai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Sheƙau ba

Dan gwagwarmayar siyasa kuma mamallakin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya ruwaito,:

"Jami'an tsaro a Cocin Dunamis sun kama yan gwagwarmaya sanya da rigar #BuhariMustGo lokacin da za su shiga Cocin don gudanar da ibada, daga baya kuma jami'an tsaron Cocin suka mika su ga hukumar DSS, wanda suke azabtar dasu a halin yanzu.
"Ina tunanin Pastor Dr Paul Eneche shima wa'azi yake akan adalci! An tafi da yan gwagwamayar su biyar a mota kirar Hilux da kuma manyan babura. Abun kunya a dakin ubangiji."

Wani ma'aikacin cocin da ya tattauna da jaridar The Punch kuma ya bukaci a boye sunan shi, lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce

"Wadannan mutanen sun yi satar shiga cocin, nace sunyi satar shiga ne saboda babu wanda yasan abun da suka shirya, babu wani bangaren na cocin da yasan wani abu a kai.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari

"Sun fito suna ihu kuma kafin ka ankara, mun gan su sanye da rigar Buhar-must-go kuma suna daukar hoton jama'a, suna nuni kamar cocin ce ta shirya zanga zanga.
"Dole mu mika su ga jami'an tsaro, saboda abu uku muka yarda da shi. Ko dai wasu ne suka turo su don tabbatar da sun saka cocin da gwamnati a rikici ko kuma su sanya aga kamar cocin ce ta dauki nauyin zanga zangar.
"Na uku shine koda suna da dalili mai karfi na yin zanga zanga, coci ba nan ne inda ya da ce ayi ta ba. In akwai matsala a kasa, aikin coci shine tayi addu'ar Allah ya taimaki shugabanni. Mun mika su ga hukumomin da ya dace don gudanar da bincike." a jawabin sa.

Har zuwa kammala wannan rahoton, babu wata sanarwa daga babban Pastor na cocin ko hukumar DSS akan lamarin.

Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Makarantar Fasto Oyedepo a Kaduna

Sojojin Nigeria a safiyar ranar Litinin sun dakile harin da aka yi yunkurin kaiwa Faith Academy, wani makarantar sakandare mallakar cocin Living Faith Church Worldwide, da Bishop David Oyedepo ya kafa.

Daily Trust ta ruwaito cewa makarantar ba shi da nisa daga makarantar kwana inda aka sace dalibai da dama a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Yan bindigan sun kai hari ne a Bether Secondary School da Faith Academy a safiyar ranar Litinin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164