An mayar da ministan Buhari da ta yanke jiki ta fadi zuwa dakin asibiti

An mayar da ministan Buhari da ta yanke jiki ta fadi zuwa dakin asibiti

  • Ambasada Maryam Yalwaji Katagum, karamar ministar masana'antu tana kwance a asibitin ATBU babu lafiya
  • Ta yanke jiki ta fadi a cikin taro yayin da za ta yi jawabi, lamarin da yasa aka gaggauta mika ta asibiti
  • Sai dai an gano cewa shugaban asibitin da kan shi ya mayar da ita dakin kwantarwa na marasa lafiya a asibitin

Karamar ministar masana'antu, cinikayya da hannun jari, Ambasada Maryam Yalwaji Katagum, wacce ta yanke jiki ta fadi a wani taro a ranar Litinin ta fara samun lafiya kuma an mayar da ita dakin asibiti dake asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.

Kamar yadda wata majiya ta sanar da Daily Trust, shugaban asibitin, Dr Yusuf Jibrin Bara ya dauka ministan da kan shi inda ya kaita dakin kwantar da marasa lafiya na asibitin.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a Zangon kataf ta Kaduna

An mayar da ministan Buhari da ta yanke jiki ta fadi zuwa dakin asibiti
An mayar da ministan Buhari da ta yanke jiki ta fadi zuwa dakin asibiti. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

CMD ya mayar da minista dakin kwantarwa

"Matsalar rashin lafiyarta karama ce kuma CMD da kanshi ya dauka ministan ya kai ta dakin kwantar da marasa lafiya," majiyar tace.

Dukkan kokarin da aka yi na jin tsokacin jami'an minsitan a kan halin da take ciki ya gagara a lokacin wallafa wannan rahoton.

Yadda minista ta yanke jiki ta fadi a taro

Ministan wacce ta je jihar Bauchi domin kaddamar da wani shiri na inganta rayuwa, ta yanke jiki ta fadi yayin da ta tashi yin jawabi inda akwai mataimakin gwamna, Sanata Baba Tela da sauransu.

KU KARANTA: Ba zan yi murabus daga siyasa ba har sai na mutu, Malam Shekarau

Da gaggawa aka mika ta asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.

"Kawai ta kama kanta ne kuma ta yanke jiki ta fadi yayin da jami'ai suka dauketa zuwa asibiti da gaggawa," wani ganau ya sanar.

Daily Trust ta tattaro cewa ministan tana Bauchi tun ranar Asabar inda ta bayyana a wani shirin kai tsaye a ranar Lahadi na gidan rediyon Globe FM

Ta dinga hidindimunta na yau da kullum kafin shirin da ta fadi na ranar Litinin.

Za a mayar da ita Abuja idan ta samu sauki

Wani babban jami'in gwamnati ya sanar da manema labarai cewa jikinta na kara samun sauki za a mayar da ita Abuja domin a cigaba da kula da ita.

A wani labari na daban, Mujahid Asari Dokubo, tsohon kwamandan tsageru kuma shugaban gwamnatin gargajiya ta Biafra, yayi martani bayan sake kama Nnamdi Kanu, shugaban IPOB da gwamnatin tarayya ta yi.

Kanu, wanda ke fuskantar tuhuma kan cin amanar kasa, ya tsallake beli bayan wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta sake shi saboda matsalar lafiya, Daily Trust ta ruwaito.

Ya tsere zuwa Ingila inda ya dinga bada umarni ga mambobin IPOB na kudu maso gabas a kan tada hazo a yankin. An sake kama shi a kasar waje kuma an dawo da shi Najeriya a ranakun karshen makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel