Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Ƙwadugo NLC

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Ƙwadugo NLC

  • Wasu yan bindiga sun samu nasarar awon gaba da shugaban ƙungiyar NLC na jihar Taraba, Peter Jediel
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun mamaye gidansa ne da safiyar Lahadi a garin Sunkani
  • Wannan shine karo na biyu da aka sace shugaban NLC na jihar Taraba, inda a baya ma wasu yan bindiga suka yi garkuwa da shi

Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da shugaban ƙungiyar ƙwadugo NLC reshen jihar Taraba, Peter Jediel, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai da dama a Kaduna

Rahotan Sahara Reporters ya bayyana cewa an sace Jediel ne a gidansa dake garin Sunkani, hedkwatar ƙaramar hukumar Ardo-Kola, jihar Taraba.

Yan Bindiga sun sace shugaban NLC na Taraba
Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Ƙwadugo NLC Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cewar ɗaya daga cikin shugabannin NLC na jihar, wanda ya tabbatar da sace shugabansa ga manema labarai ta wayar salula, maharan sun mamaye gidan Jediel ne da sanyin safiyar Lahadi.

Yace: "Waɗanda duka yi garkuwa da Mr. Jediel sun tuntuɓi iyalansa, kuma sun nemi a biya su kuɗin fansa kafin su sako shi."

KARANTA ANAN: Gwamna Masari Ya Rushe wasu Gine-Gine a Jiharsa, Yace Sun Saɓa Wa Doka

Iyalan Jediel sun tabbatar da sace ɗan uwansu

Wata majiya daga cikin iyalan shugaban NLC ta Taraba, Jediel, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Majiayar ta bayyana cewa maharan sun sace Jediel a gidansa dake garin Sunkani, ƙaramar hukumar Arɗo-Kola da misalin ƙarfe 12:30 da daren ranar Lahadi.

Legit.ng hausa ta gano cewa wannan shine karo na biyu da yan bindiga suka sace Shugaban NLC-Taraba.

A wani labarin kuma Bayan Shekara 245 da Samun Yanci, Shugaba Buhari Ya Aike da Saƙon Murna Ga Shugaba Biden

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ya aike da saƙon murna ga shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, yayin da ƙasarsa ke murnar cika shekaru 245 da samun yancin kai ranar 4 ga watan Yuli.

Buhari ya bayyana cewa ƙasashen Najeriya da Amurka sun haɗu a ɓangarori da dama kamar Demokaraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel