Gwamna Masari Ya Rushe wasu Gine-Gine a Jiharsa, Yace Sun Saɓa Wa Doka

Gwamna Masari Ya Rushe wasu Gine-Gine a Jiharsa, Yace Sun Saɓa Wa Doka

  • Gwamnatin jihar Katsina, ta rushe wasu gine-gine a ƙaramar hukumar Ɓatagarawa
  • Gwamnatin tace sai da ta baiwa waɗanda suke da mallakin wurin wa'adin lokaci su tattara kayansu
  • A cewarta, gine-ginen sun saɓa wa doka, domin sun shiga hanya kuma hakan yasa ba'a amfani da wurin

Hukumar tsara birane da karkara ta jihar Katsina, (URPB) ta rushe wasu gine-gine da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba a yankin Morawa, ƙaramar hukumar Ɓatagarawa, jihar Katsina, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai da dama a Kaduna

Kakakin ma'aikatar ƙasa ta jihar, Alhaji Yakubu Lawal, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi a Katsina.

Lawal ya bayyana cewa an gudanar da rusau ɗin ne bisa jagorancin, Abdullahi Gide-Abubakar, shugaban tsare-tsare na hukumar URPB, kamar yadda pm news ta ruwaito.

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari
Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, Ya Fara Rusau a Jiharsa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa an rushe gine-ginen ne bayan wa'adin da aka baiwa masu wajen na su tattara kayan su ya cika.

Yace: "Kafin rushe ginin sai da muka sanar da masu wurin da su tashi kafin wa'adin da muka basu, amma suka ƙi bin umarni."

"Mun gano masu wurin sun shiga hanya, wanda hakan yasa suka hana mutane amfani da hanyar yadda ya kamata."

"Shiga kan hanya ya saɓa wa dokokin hukumar URPB, saboda haka yasa aka rushe wurin kamar yadda dokar ta tanazar."

Gwamnati ba zata ƙyale duk wani gini da ya saɓa wa tsarin doka ba

Jim kaɗan bayan kammala rusau, shugaban tawagar da suka gudanar da aikin ya jaddada cewa gwamnati ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen ɗaukar mataki ƙan duk abinda ya saɓa wa doka.

Ya bayyana cewa hukumar URPB ba zata gajiya ba har sai ta tabbatar da anbi tsari mai kyau a birane da karkara.

KARANTA ANAN: Bayan Shekara 245 da Samun Yanci, Shugaba Buhari Ya Aike da Saƙon Murna Ga Shugaba Biden

Lawal yayi kira ga al'ummar jihar Katsina da su rinƙa neman izinin gwamnati kafin su yi gini musamman a kusa da kan hanya.

A wani labarin kuma Kada Ku Sassauta Har Sai Kun Yi Kaca-Kaca da Yan Ta'addan Najeriya Baki Ɗaya, COAS Ga Sojoji

Hafsan sojin ƙasa, COAS Farouk Yahaya, ya umarci sojojin dake yaƙi da ta'addanci da cewa kada su sassauta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Manjo Yahaya ya faɗi hakane a wurin taron murnar zagayowar ranar sojojin Najeriya (NADCEL) 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel