Yanzu-Yanzu: Ministan Shugaba Buhari Ta Yanke Jiki Ta Faɗi a Wurin Taro

Yanzu-Yanzu: Ministan Shugaba Buhari Ta Yanke Jiki Ta Faɗi a Wurin Taro

  • Karamar ministan kula da ma'aikatu ta ƙasa, Maryam Katagun, ta yanke jiki ta faɗi a wurin wani taro a Bauchi
  • Ministan ta kasance a jihar Bauchi tun ranar Asabar, inda ta gudanar da wasu ayyuka kafin taron na ranar Litinin
  • Wani jami'in gwamnati ya bayyana cewa da zaran ta samu sauƙi zata koma Abuja don cigaba da duba lafiyarta

Ƙaramar minitan ma'aikatun kasuwanci da hannun jari, Maryam Yalwaji Katagun, ta yanke jiki ta faɗi a wurin wani taro a jihar Bauchi ranar Litinin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Ƙwadugo NLC

Ministan, wanda taje Bauchi domin ƙaddamar da wani shirin bada tallafi, ta yanke jiki ta fafi ne yayin da take ƙoƙarin jawabinta ga mahalarta taron, wanda mataimakin gwamna, Sanata Baba Tela, yana wurin.

Maryam Katagun
Yanzu-Yanzu: Ministan Shugaba Buhari Ta Yanke Jiki Ta Faɗi a Wurin Taro Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Rahoton vanguard ya bayyana cewa, an gaggauta ɗaukar ministan zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa Bauchi (ATBU-TH).

"Ba zato ba tsammani ta riƙe ƙanta, ta faɗi ƙasa a hankali, yayin da jami'ai suka yi gaggawar ɗaukarta zuwa Asibiti." inji wani shaidan gani da ido.

Ministan ta kai ziyarar aiki Bauchi tun ranar Asabar

Legit.ng hausa ta gano cewa ministan, wanda ta kasance a jihar Bauchi tun ranar Asabar, ta yi fira da gidan radiyon Globe FM a wani shirin kai tsaye ranar Lahadi.

Hakanan kuma ta gudanar da wasu ayyukan tun bayan zuwanta jihar kafin taron ƙaddamar da tallafi ranar Litinin.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai da dama a Kaduna

Duk wani ƙoƙari na jin halin da take ciki a cibiyar kula da masu rauni na ATBU-TH yaci tura.

Amma wani babban jami'in gwamnati ya shaidawa manema labarai cewa da zaran ta samu sauƙi zata koma Abuja domin a cigaba da kulawa da lafiyarta.

A wani labarin kuma Barazanar Tsaro a Abuja, FCTA Ta Rushe Gine-Gine Sama da 400 a Kan Hanyar Filin Jirgi

FCTA ta rushe wasu gine-giɓe da runfuna da aka kafa sama da 400 a kan hanyar filin jirgin Nnamdi Azikwe.

Tace ta ɗauki wannan matakin ne domin kare al'ummar birnin tarayya tare da dukiyoyinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel