Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai da dama a Kaduna

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai da dama a Kaduna

  • Wasu yan bindiga sun kutsa makarantar Bethel Baptist da daren ranar Litinin, inda suka yi awon gaba da ɗalibai
  • Wani mazaunin yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace bai san adadin yawan ɗaliban da aka sace ba
  • Ya bayyana cewa maharan sun harbi sojoji guda biyu, amma bai san halin da jami'an ke ciki ba a yanzun

Yan bindiga a ranar Litinin, sun yi awon gaba da ɗalibai da dama a makarantar sakandiren kwana ta Bethel Baptist dake Maraban Rido, ƙaramar hukumar Chukun, jihar Kaduna.

KARANTA ANAN: Bayan Shekara 245 da Samun Yanci, Shugaba Buhari Ya Aike da Saƙon Murna Ga Shugaba Biden

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Leadership.

Yace yan bindigan sun mamaye makarantar da misalin.ƙarfe 2:00 na dare, inda suka fara harbi a sama kafin daga bisani su sace ɗaliban, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.

Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai a Kaduna
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba da Ɗalibai da dama a Kaduna Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A cewarsa, maharan sun yi awon gaba da ɗalibai da dama, amma huɗu daga ciki sun tsere sun koma makaranta.

Yace: "A yayin harin, yan bindigan sun harbi sojoji guda biyu, amma bansani ba ko sun mutu ko suna raye."

"Zai yi wahala in faɗi adadin ɗaliban da aka sace amma dai suna da yawa."

KARANTA ANAN: Kada Ku Sassauta Har Sai Kun Yi Kaca-Kaca da Yan Ta'addan Najeriya Baki Ɗaya, COAS Ga Sojoji

Hukumar yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, ta bayyana cewa maharan sun tafi da ɗalibai 17.

A wani labarin kuma Gwamna Masari Ya Rushe wasu Gine-Gine a Jiharsa, Yace Sun Saɓa Wa Doka

Hukumar tsara birane da karkara ta jihar Katsina , (URPB) ta rushe wasu gine-gine da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba a yankin Morawa, ƙaramar hukumar Ɓatagarawa.

Kakakin ma'aikatar ƙasa ta jihar, Alhaji Yakubu Lawal, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi a Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel