Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana yadda suka fara

Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana yadda suka fara

  • asu ma'aurata sun bayyana farin ciki a kafar facebook, yayin da ake taya su murnar biki
  • Ma'auratan sun hadu a farko a kafar Facebook, lamarin da ya kai ga auren soyayya tsakaninsu
  • Angon ya bayyana cewa, matar ce ta fara yi masa magana don sanin inda yake, karshe dai suka yi aurensu

Duniyar Soyayya - Shafukan sada zumunta sun wuce inda mutane suke cudanya domin samun nishadi, shafuka ne da a yanzu suke hada aure tsakanin masoya da kulla alaka mai karfi.

Wasu ma'aurata 'yan Najeriya da suka hadu a Facebook sun bayyana yadda suka samu farin ciki a yanar gizo da kyawawan hotuna daga bikin aurensu na gargajiya.

Sakon da mutumin mai suna Okello Peters Izuchukwu ya bayyana a shafin Facebook yadda ya hadu da matarsa yana cewa:

"'Yadda abin ya faro da yadda abin yake ''

Izuchukwu ya nuna hotuna guda biyu daga tattaunawarsa ta farko da matar tasa mai suna Udo Dirim.

KARANTA WANNAN: Cikakken Bayani: Yadda Tankar Gas Ta Fadi a Kasuwa, Ta Yi Kaca-Kaca da Mutane 10

Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana firarsu ta farko
Wurin Biki | Hoto: Udo Dirim
Asali: UGC

Udo ce da farko ta fara yunkurin saninsa lamarin da ya rikide zuwa dangantaka mai karfi da ya kai ga aure a yanzu.

Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana yadda suka fara
Rubutun da ya wallafa | Hoto: Okello Peters Izuchukwu
Asali: Facebook

Mutane sun jinjinawa matar saboda fara yi masa magana da farko

Jama'a a yanar gizo sun yaba wa matar saboda samun kwarin gwiwar yi wa mutumin da yake bako a wurinta magana a farko idan aka kwatanta da wasu matan da ke jin sun fi karfin magana da saurayi da farko.

Peter Oshun ya ce:

"Don haka ita ta fara maka magana ma...Ina taya ta matukar murna, kuma ina muku fatan rayuwar aure mai ni'ima."

Erich Uchenna Chimara yayi sharhi:

"Da gani kun dace. Yarinyar ce ta yi karfin halin magana dashi kuma ta gabatar da kanta."

Steve Chike Abia ya rubuta:

"Wata yarinya ta kasance a akwatin sako na tana ta 'Barka', 'Ina lafiya' kawai. A tunaninta ta yi kamu. Ta fi karfin ta turo sako mai amfani. Yanzu ga wata ta dace."

Joy Ekenyong ya ce:

"Abin dariya ne yadda muke yin abubuwa ba mu san yanayin da zai dauka ba da yadda rayuwarmu za ta iya canzawa ta dalilin haka.
"Yana da kyau sosai ka karanta wannan, a yammacin yau ...
"Ina tayaku da sake taya ku murna gaba daya."

Kalli hotunan bikin:

Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana firarsu ta farko
Wurin biki: | Hoto: Udo Dirim
Asali: Facebook

Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana firarsu ta farko
Wurin biki: | Hoto: Udo Dirim
Asali: UGC

Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana firarsu ta farko
Wurin biki: | Hoto: Udo Dirim
Asali: Facebook

Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana firarsu ta farko
Wurin biki: | Hoto: Udo Dirim
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: 'Yar Shugaba Buhari Ta Ciri Tuta, Ta Yi Digirgir a Daukar Hoto a Kasar Waje

A wani labarin, Wata budurwa 'yar Najeriya ta gigita kafafen sada zumunta bayan ta amince da tayin auren saurayinta.

Matar mai amfani da @swiss_scarlet a Instagram, ta wallafa wani bidiyo inda saurayinta ya gwangwajeta da N2.5 miliyan saboda ta amince da tayin aurensa.

Kamar yadda Instabog9ja ta tabbatar, budurwar masaniya ce a fannin hada mayuka. A wani bidiyo dake yawo, an boye fuskar saurayin sai dai hannunsa kadai ake iya gani inda yake zuba mata ruwan lemu a kofi tare da saka mata zobe a hannu.

Budurwar cike da jin dadi tare da annashuwa ta nuna mamakinta game da dunkulin kudin da aka bata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel