'Yar Shugaba Buhari Ta Ciri Tuta, Ta Yi Digirgir a Daukar Hoto a Kasar Waje

'Yar Shugaba Buhari Ta Ciri Tuta, Ta Yi Digirgir a Daukar Hoto a Kasar Waje

  • 'Yar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kammala karatun digirin digir-gir a kasar waje
  • An ruwaito cewa, ta kammala karatun ne a fannin daukar hoto, cikin hotuna abin ban sha'awa
  • A baya ta kammala karatun ta a kasar Ingila, in da ta kammala da sakamako mai matukar kyau

Hanan ‘yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta samu digiri na biyu a fannin daukar hoto.

Bayo Omoboriowo, mai daukar hoto na musamman ga shugaba Buhari ne ya sanar da hakan a wani hoton bidiyo inda yake taya ta murna, The Cable ta ruwaito.

Ba a bayyana ko wace jami'a ce ta kammala digirin ba amma faifan bidiyon ya nuna tana tafe kan dandamali tare da wasu fararen malamanta da ke ba ta lambar yabo.

Hanan ta taka rawar gani a karatun nata, a baya ta kammala karatunta a jami’ar Ravensbourne a kasar Ingila.

KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai Ta Tabbatar da Nadin Manjo Faruk Yahaya

'Yar Shugaba Buhari Ta Ciri Tuta, Ta Kammala Digirin Digirgir a Ilimin Daukar Hoto
'Yar Shugaba Buhari da 'yan uwa | Hoto: topnaija.ng
Asali: UGC

An haife ta a shekarar 1998, Hanan ta fara karatun ta a makarantar Kaduna International School. Ta ci gaba da karatu a fannin daukar hoto da kafofin watsa labarai, ta kammala da sakamakon kololuwa a karatunta.

Bayan kammala karatun ta a Ingila, Hanan ta dawo gida Najeriya a shekarar 2019 domin ta zama mai daukar hoto.

A shekarar 2020, diyar shugaban kasa ta yi aure da Mohammad Turad Sha’aban, dan Mahmud Sani Sha’aban, tsohon dan majalisa da ya wakilci Zariya a majalisar wakilai daga Mayu 2003 zuwa Mayu 2007.

Gwamnoni sun isa fadar sarkin Kano don tsara bikin Yusuf Buhari

Kafin bayyanar hotunan Hanan, a jiya ne gwamnoni da ministoci suka isa fadar mai martaba Sarkin Kano don tsara tsare-tsaren bikin auren Yusuf Buhari, dan shugaban kasa, Daily Trust ta ruwaito.

Yusuf na shirin auren diyar Sarkin Bichi kuma tawagar da ke karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa sun je Kano don tsara tsare-tsaren bikin auren.

Sarkin na Bichi kane ne ga Sarkin Kano, wanda shi ya karbi bakuncin wakilai daga fadar ta shugaban kasa.

Bidiyon saurayin da ya baiwa budurwa kyautar N2.5m saboda ta amince zata aure shi

A wani labarin, Wata budurwa 'yar Najeriya ta gigita kafafen sada zumunta bayan ta amince da tayin auren saurayinta.

Matar mai amfani da @swiss_scarlet a Instagram, ta wallafa wani bidiyo inda saurayinta ya gwangwajeta da N2.5 miliyan saboda ta amince da tayin aurensa. Kamar yadda Instabog9ja ta tabbatar, budurwar masaniya ce a fannin hada mayuka.

A wani bidiyo dake yawo, an boye fuskar saurayin sai dai hannunsa kadai ake iya gani inda yake zuba mata ruwan lemu a kofi tare da saka mata zobe a hannu. Budurwar cike da jin dadi tare da annashuwa ta nuna mamakinta game da dunkulin kudin da aka bata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel