'Yan bindiga sun kai hari Katsina, sun wawashe shagon cajin wayoyi

'Yan bindiga sun kai hari Katsina, sun wawashe shagon cajin wayoyi

  • Wasu 'yan bindiga sun farmaki wani yankin jihar Katsina, sun hallaka mutum daya sun jikkata wasu
  • An ce sun shiga shagon wani mai cajin wayar salula, suka kwashe komai da ke cikin shagon
  • Hakazalika an yi jana'izar wanda ya mutu an kuma zarce da wanda ji wa rauni zuwa asibiti

Mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu hudu suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari garin Danmusa, karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan sanda sun kawo agajin gaggawa kuma sun dakile harin wanda ya dauki kimanin minti 40, yayin da maharan suka wawushe wani kantin cajin wayar salula.

Majiyar ta ce maharan sun zo ne da misalin karfe 8:30 na daren ranar Asabar suka fara harbin kan mai uwa da wabi a garin, inda suka kashe mutum daya kuma suka ji wa daya rauni, ta kara da cewa an yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

KARANTA WANNAN: Bayan shan ragargaza daga sojoji, Boko Haram da ISWAP sun sanyawa jama'a haraji

'Yan bindiga sun kai hari Katsina, sun wawashe shagon cajin wayoyi
Wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

A cewar majiyar:

“Saurin dauki da hukumomin tsaro suka kawo ya taimaka wajen fatattakar maharan.
"Ba su samu yin garkuwa da kowa ba, sai shagon wayar salula daya da suka kwashe duk wayoyin da mutane suka kawo don cajin batirinsu."

Ta ce mutane hudun da suka jikkata suna karbar kulawa a Babban Asibitin Danmusa.

Yunkurin jin ta ‘yan sanda game da lamarin a lokacin rubuta rahoton ya ci tura saboda Kakakin rundunar 'yan sanda a Katsina, SP Gambo Isah, ba ya amsa kira.

KARANTA WANNAN: Cikakken Bayani: Yadda Tankar Gas Ta Fadi a Kasuwa, Ta Yi Kaca-Kaca da Mutane 10

An Cafke Wasu 'Yan Bindiga Bayan Karbar Kudin Fansa Da Kashe Wanda Suka Sace

A wani labarin, Jami’an ‘yan sanda a jihar Abia sun cafke gungun 'yan bindiga, wadanda suka kware a harkar satar mutane tare da neman kudin fansa, Channels Tv ta ruwaito.

Fiye da mutane takwas da ake zargi jami’an tsaro na jihar suka cafke, an ce biyu daga cikinsu sun kashe wanda suka sace bayan sun karbi kudin fansa na naira dubu dari bakwai (N700,000).

An kuma ce sun sayar da mota kirar Lexus ta mutumin da suka kashen a kan kudi naira dubu dari biyu (N200,000).

A yayin zantawa da manema labarai a Umuahia, Kwamishinar 'yan sanda, Janet Agbede ta ce tsagerun sun kasance cikin binciken 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a jihar a cikin 'yan kwanakin nan bisa aiwatar da fashi da makami da ayyukan satar mutane a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel