Cikakken Bayani: Yadda Tankar Gas Ta Fadi a Kasuwa, Ta Yi Kaca-Kaca da Mutane 10

Cikakken Bayani: Yadda Tankar Gas Ta Fadi a Kasuwa, Ta Yi Kaca-Kaca da Mutane 10

  • Wata tankar mai ta fadi a wani yankin jihar Oyo, inda ta hallaka akalla mutane 10
  • An ruwaito cewa, tankar ta kubce wa direban ne, kuma ya gagara sarrafa ta a hanya
  • An ce rundunonin jami'an tsaro sun halarci inda lamarin ya faru domin kawo dauki

Wata tankar dakon gas ta murkushe mutane 10 tare da jikkata wasu a wata kasuwa a garin Ibadan.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa motar ta kwace wa direban ne a kusa da yankin Idi Arere kuma ya yi ta kokarin sarrafata har sai da ta isa Kasuwar Bode.

An ce jami'an kashe gobara sun isa wurin don hana tankar da ta kife daga fashewar da kamawa da wuta.

KARANTA WANNAN: An Cafke Wasu 'Yan Bindiga Bayan Karbar Kudin Fansa Da Kashe Wanda Suka Sace

Da Duminsa: Tankar Mai Ta Fadi a Kasuwa, Ta Yi Kaca-Kaca da Mutane
Wata tankar gas da ta fadi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Amma mazauna garin sun ce har yanzu suna cikin yanayin tsoro saboda yiwuwar fashewar wani abu daga tankar.

Wani shaidaN gani da ido ya fadawa SaharaReporters cewa hukumomin tsaro sun mamaye kasuwar domin kwashe gawarwakin wadanda hadarin ya rutsa da su.

Ya ce:

"Abinda ya faru yanzun nan, mun kirga gawarwaki goma a kasa tuni. Tankar mai ce ta kubce a Idi-Arere ta shiga kasuwar Bode."

Kwamandan bangare na hukumar kiyaye haddura ta kasa a jihar Oyo, Uche Chukwurah, ba a samu damar jin ta bakinsa game da hatsarin ba.

Wasu daga cikin yan kasuwan yankin da suke wurin lokacin da hatsarin ya afku sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safe.

Sun kara da cewa faduwar da motar tayi lokacin da ta afka cikin wani rukunin shaguna da ke cikin kasuwar ya haifar da fargaba, Nigeria Tribune ta tattaro.

KARANTA WANNAN: Jerin Manyan Jami'ai 14 da Shugaban Hafsun Soji Ya Nada Bayan Tabbatar Dashi

Fasinjoji Sun Makale a Daji Bayan da Jirgin Kasa Ya Lalace a Kaduna

A wani labarin, Daruruwan fasinjoji da ke cikin jirgin kasa na Abuja/Kaduna a yanzu haka sun makale a Dutse, yankin Kaduna, yayin da jirgin yasamu nakasu 'yan mintoci da fara tafiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa minti biyar bayan jirgin ya tashi daga Tashar Rigasa da ke Kaduna, sai ya samu matsalar inji. Sau biyu, jirgin ya tsaya kafin ya isa Dutse, inda daga karshe ya lalace.

Midat Joseph, mataimakin Sakatare na kasa na kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), wanda na daya daga cikin fasinjojin, ya ce jirgin ya samu matsala ne da misalin karfe 7 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel