An Cafke Wasu 'Yan Bindiga Bayan Karbar Kudin Fansa Da Kashe Wanda Suka Sace

An Cafke Wasu 'Yan Bindiga Bayan Karbar Kudin Fansa Da Kashe Wanda Suka Sace

  • Rundunar 'yan sanda sun cafke wasu da ake zargin 'yuan bindiga ne masu sace mutane
  • Sun amsa laifin cewa, sun sace wani mutum, sun hallaka shi bayan karbar kudin fansa
  • An kame su dauke da muggan makamai da kuma wayar mutumin da suka sace suka hallaka

Jami’an ‘yan sanda a jihar Abia sun cafke gungun 'yan bindiga, wadanda suka kware a harkar satar mutane tare da neman kudin fansa, Channels Tv ta ruwaito.

Fiye da mutane takwas da ake zargi jami’an tsaro na jihar suka cafke, an ce biyu daga cikinsu sun kashe wanda suka sace bayan sun karbi kudin fansa na naira dubu dari bakwai (N700,000).

An kuma ce sun sayar da mota kirar Lexus ta mutumin da suka kashen a kan kudi naira dubu dari biyu (N200,000).

A yayin zantawa da manema labarai a Umuahia, Kwamishinar 'yan sanda, Janet Agbede ta ce tsagerun sun kasance cikin binciken 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a jihar a cikin 'yan kwanakin nan bisa aiwatar da fashi da makami da ayyukan satar mutane a jihar.

KARANTA WANNAN: Najeriya Ta Hada Kai da Majalisar Dinkin Duniya Don Samarwa Kasa Abinci Mai Kyau

Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke 'Yan Bindigan dake Karbar Kudin Fansa Kuma Su Kashe Mutum
Wadanda aka cafke da kayayyakin da aka kame | Hoto:channelstv.com
Asali: UGC

An bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka Samuel Udochukwu, mai shekaru 26 da Emeka Okedum, dan asalin karamar hukumar Osah Ukwu Obingwa, jihar Abia.

Sai kuma Udo Onwukwe, mai shekaru 48 daga karamar hukumar Urnuonu Obingwa, jihar Abia, wanda har zuwa kama su shi ne mai ba da makamai da samar da sansani ga 'yan ta'addan.

Sauran sune: Okechukwu Obioma, dan shekaru 31, daga karamar hukumar Umual Ntigha Obingwa, mai gadin wadanda abin ya sace; Saviour Akpan, mai shekaru 27 daga lkoro Esenan a karamar hukumar Orukanam, ta jihar Akwa Ibom, shine direban 'yan bindigan.

Sauran mambobin sun hada da Abia Daniel, mai shekaru 41 daga Item a karamar hukumar Bende Lardin Abia, da Kelechi Nnachi, mai shekaru 24 daga Edda a karamar hukumar Afikpo ta Kudu, jihar Ebonyi.

Abubuwan da aka kwato daga hannun ‘yan bindigan sun hada da bindiga kirar AK-47 guda daya mai lamba TC 6664 tare da harsasai 25, karamar bindiga mai dauke da harsasai goma, da bindiga kirar gida da mota.

An kuma kwato wayar wanda suka sace kirar Techno Spark da dai sauran kayayyaki.

A cewar shugaban 'yan sandan na jihar Abia, bayanai masu amfani da masu bincike suka samu ne ya kai ga cafke 'yan bindigan.

KARANTA WANNAN: Abu Kamar Wasa: Yadda Yara 10 Suka Bakunci Lahira Bayan Cin Tuwon Dawa

Kwamishinan na Abia ya gargadi matasa wadanda suke ganin aikata laifi a matsayin hanyar samu da su daina ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Bayan Harbe Mata Mai Juna Biyu da Sace Mijinta, 'Yan Bindiga Sun Nemi Fansa N3Om

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wata mata mai juna biyu a jihar Kwara sun nemi a ba su kudin fansa na Naira miliyan 30 ga mijinta da suka sace, The Nation ta ruwaito.

‘Yan bindigar sun harbe matar mai juna har lahira sannan suka yi garkuwa da mijinta a ranar Asabar din da ta gabata a Offa, cikin karamar hukumar Offa ta jihar Kwara.

Wata majiya daga dangin wadanda masifar ta rutsa dasu ta tabbatar da hakan a ranar Litinin, inda ta ce sun sami damar tara Naira miliyan biyu.

Majiyar ta ce:

“Sun nemi iyalin su biya Naira miliyan 30 kudin fansa kafin mu samu a sako shi. Amma mun sami damar tara Naira miliyan biyu ne kawai wanda suka ki karba.
"Mun riga mun rasa uwa mai juna biyu, Hawa wacce harsashi ya buge ta lokacin da masu garkuwar ke harbi ba kakkautawa yayin barnar."

A baya, wasu ‘yan bindiga, a ranar Asabar, sun harbe wata mata mai ciki har lahira tare da yin garkuwa da mijinta a karamar hukumar Offa da ke Jihar Kwara.

Marigayiyar, wacce wasu majiyoyi suka bayyana sunanta da Hawa, matar Lukman Ibrahim, wani dillalin wayar salula a Kasuwar Owode wanda aka fi sani da "LUKTECH".

Lamarin, ya faru ne a daren Asabar 'yan mintoci kadan kafin karfe 7 na yamma yayin da Lukman ke tuka surukinsa, matarsa ​​mai juna biyu da yaronsu zuwa gida a kan hanyar Ojoku, kusa da Hedikwatar 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel