Ba Zan Taɓa Mantawa da Fasto Tunde Bakare ba, El-Rufa'i Ya Faɗi Alƙarsa da Faston Coci

Ba Zan Taɓa Mantawa da Fasto Tunde Bakare ba, El-Rufa'i Ya Faɗi Alƙarsa da Faston Coci

  • Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana kyakkyawar alaƙar dake tsakaninsa da Fasto Tunde Bakare
  • Gwamnan yace Fasto Bakare, shine ya gabatar da shi ga shugaban ƙasa Buhari da jam'iyyar CPC a baya
  • El-Rufa'i ya musanta zargin da wasu ke masa cewa yana ɗa tsattsauran ra'ayin jihadi

Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya bayyana alaƙar dake tsakninsa da Fasto Tunde Bakare na cocin addinin kirista, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

El-Rufa'i, yace Fasto Bakare shine ya gabatar da shi ga shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da tsohuwar jam'iyyarsa wato CPC.

KARANATA ANAN: Da Ɗuminsa: Bayan Komawarsa APC, Gwamna Matawalle Ya Sallami Dukkan Mashawartansa Na Musamman

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin wata fira da yayi da sashin BBC na yaren Fijin, wanda ya gudana a Kaduna.

Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i
Ba Zan Taɓa Mantawa da Fasto Tunde Bakare ba, El-Rufa'i Ya Faɗi Alƙarsa da Faston Coci Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Malam Nasiru ya musanta zargin da wasu suke masa cewa ɗan jihadi ne, kuma ɗan fulani ne mai tsattsauran ra'ayi.

Gwamnan yace: "Ɗaya daga cikin mutanen da suka taka rawa a rayuwata, kuma ɗaya daga cikin wadanda nike ganin girmansu a siyasa shine Fasto Tunde Bakare."

"A zahirin gaskiya, Fasto Bakare ne ya gabatar da ni ga shugaba Buhari da kuma CPC. Idan ni ɗan jihadi ne ta ya Fasto Bakare zai haɗa alaƙa da ni?"

Ni musulmi ne amma ba mai tsattsauran ra'ayin jihadi ba

Gwamna El-Rufa'i ya ƙara da cewa ana kirana da sunaye da dama kamar cewa ni ɗan ƙabilar Hausa-Fulani ne mai tsattsauran ra'ayi ko ni ɗan jihadi ne, amma ba haka bane.

Yace: "Suna kira na da sunaye da dama, sun ce ni Hausa-Fulani ne, ni ɗan jihadi ne, yaushe na zama ɗan jihadi? Kuma a ina? Ba ni da cikakkiyar rijistar zama ɗan wata ƙungiyar addinin musulunci."

KARANATA ANAN: Ba da Jimawa Ba Wasu Gwamnonin PDP Zasu Biyo Mu Zuwa APC, Gwamna Ya Faɗi Lokaci

"Ni musulmi ne kuma cikakken mabiyin addinin musulunci, amma na yi imani cewa addini wata mas'ala ce ta kai-da-kai, ko a ofiishina na gwamna idan lokacin sallah yayi ina fita ne kamar lokacin da zan biya wata buƙata tawa."

"Bana cewa kowa ya zo muyi sallah tare, saboda kowa ƙabarinsa daban. Idan kuka duba makusanta na a gwamnati zaku ga ba musulmai kaɗai bane."

A wani.labarin kuma Ministan Buhari Ya Ɓalle Daga Jam'iyyar APC, Ya Buɗe Sabuwar Sakateriya a Jiharsa

Jam'iyyar APC a jihar Kwara ta dare gida biyu, inda ministan yaɗa labaru, Lai Muhammed ya buɗe sabuwar sakateriya, kamar yadda punch ta ruwaito.

Rikicin cikin gida a jam'iyya mai mulkin Kwara ya fara ne tun bayan zargin da gwamna yayi wa wasu jiga-jigan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel