Ba da Jimawa Ba Wasu Gwamnonin PDP Zasu Biyo Mu Zuwa APC, Gwamna Ya Faɗi Lokaci

Ba da Jimawa Ba Wasu Gwamnonin PDP Zasu Biyo Mu Zuwa APC, Gwamna Ya Faɗi Lokaci

  • Gwamnan Ebonyi, David Umahi, yace akwai takwarorinsa gwamnonin PDP da zasu sauya sheƙa zuwa APC ba da jimawa ba
  • Gwammnan wanda bai daɗe da komawa jam'iyya mai mulki ba yace ba zasu bari APC ta faɗi ba
  • Yace ƙalubalen tsaron da ake fama da shi a jiharsa na da alaƙa da rashin haɗin kan jiga-jigan APC na jihar

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa akwai wasu takwararonsu gwamnonin PDP da zasu sauya sheƙa zuwa APC ba da jimawa ba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wata Sabuwa: Ministan Buhari Ya Ɓalle Daga Jam'iyyar APC, Ya Buɗe Sabuwar Sakateriya a Jiharsa

Gwamnan ya faɗi hakane a wurin taron jiga-jigan jam'iyyar APC na jihar, wanda aka shirya domin tattaunawa kan yadda za'a gudanar da tarukan APC dake tafe a jihar.

Umahi, wanda bai jima sosai da sauya sheƙa zuwa APC ba, ya tabbatar da cewa ba zai bari a ƙayar da jam'iyyar a jihar Ebonyi ba.

Gwamnan Ebonyi, David Umahi
Ba da Jimawa Ba Wasu Gwamnonin PDP Zasu Biyo Mu Zuwa APC, Gwamna Ya Faɗi Lokaci Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace: "Muna samun cigaba, kuma muna aiki tuƙuru muga ta yadda gwamnatin tarayya zata kawo mana agaji. Ba zamu bari APC ta sha ƙasa a jihar Ebonyi ba."

"Akwai sauran Gwamnonin PDP da zasu sauya sheƙa zuwa APC a watanni kaɗan masu zuwa."

KARANTA ANAN: Yadda Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i Ya Cire Ɗansa Daga Makarantar Gwamnati a Sirrince

Umahi ya roƙi haɗin kai tsakanin jiga-jigan APC

Gwamna Umahi ya zargi matsalolin tsaron da jihar ke fama da shi da rashin haɗin kan masu faɗa aji na jam'iyyar APC da kuma son kai dake tsakanin su.

Gwamnan yace matuƙar aka ɗinke wannan ɓarakar da ta kunno kai to APC zata cigaba da samun nasara kamar yadda aka santa da hakan.

A wani Labarin kuma Bayan Ganawa da Nnamdi Kanu, Lauya Ya Faɗi Halin da Ya Shiga Kafin a Dawo da Shi Najeriya

Ifeanyi Ejiofor, lauyan dake kare shugaban haramtacciyar ƙungiyar taware IPOB, Kanu, ya samu ganawa da shi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Lauyan ya bayyana cewa an damƙe wanda yake karewa tun 18 ga watan Yuni, inda aka tsare shi tare da azabtarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262