Wata Sabuwa: Ministan Buhari Ya Ɓalle Daga Jam'iyyar APC, Ya Buɗe Sabuwar Sakateriya a Jiharsa

Wata Sabuwa: Ministan Buhari Ya Ɓalle Daga Jam'iyyar APC, Ya Buɗe Sabuwar Sakateriya a Jiharsa

  • Jam'iyyar APC a jihar Kwara ta dare gida biyu, inda ministan yaɗa labaru, Lai Muhammed ya buɗe sabuwar sakateriya
  • Rikicin cikin gida a jam'iyya mai mulkin Kwara ya fara ne tun bayan zargin da gwamna yayi wa wasu jiga-jigan jihar
  • Muhammed yace za'a sake gudanar da rijistar zama ɗan APC a jihar saboda ba su amince da ta baya ba

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ɓalle daga jam'iyyar APC ta jihar Kwara, inda ya bayyana cewa bada jimawa ba za'a canza rijistar yan jam'iyya a jihar, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan Ganawa da Nnamdi Kanu, Lauya Ya Faɗi Halin da Ya Shiga Kafin a Dawo da Shi Najeriya

Muhammed, wanda yayi jawabi a wurin buɗe sabuwar sakateriyar APC ta ɓangarensa a Ilorin, ranar Asabar, yace rijistar yan jam'iyyar da aka gudanar a jihar ba mai inganci bace, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar da kuma ɓangaren ministan yaɗa labaru sun gudanar da gangami daban-daban na murnar cikar APC shekara biyu a kan mulki.

Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Muhammed
Wata Sabuwa: Ministan Buhari Ya Ɓalle Daga Jam'iyyar APC, Ya Buɗe Sabuwar Sakateriya a Jiharsa Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yayin da ɓangaren gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman Abdulrazaq, yake da sakateriyar jam'iyya a yankin Tanke, ɓangaren minista Lai ya ƙaddamar da tasa sakateriyan a GRA, Ilorin.

Muhammed, yace: "An sanya son rai a rijistar zama ɗan jam'iyya da aka gudanar ba da jimawa ba saboda mafi yawancin mambobin APC ba su samu damar yin rijista ba."

"Lokacin da muka gano haka, da ni da tsofaffin yan takarar gwamna biyu, farfesa Oba AbdulRaheem da Alhaji Tajudeen Audu, sai muka garzaya wurin uwar jam'iyya ta ƙasa."

"Mun je mun faɗawa shugaban kwamitin riƙo, Mai Mala Buni, kuma ya tabbatar mana da cewa za'a sake gudanar da rijista a jihar."

Gwamnan Kwara ya zargi manyan APC da karkatar da kuɗi

A ranar 26 ga watan Yuni, Gwamna AbdulRazaq, ya zargi jiga-jigan APC na jihar cewa sun karɓi maƙudan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe a 2019, amma ko sisi ba su kawo masa ba.

KARANTA ANAN: Yadda Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i Ya Cire Ɗansa Daga Makarantar Gwamnati a Sirrince

Amma Lai Muhammed ya fito ya musanta wannan zargin, ya bayyana cewa babu wani gwamna ko minista da ya bashi sisin kobo tallafin yaƙin neman zaɓe a 2019.

"Ban karkatar da ko naira ba daga cikin kuɗin yaƙin neman zaɓen APC a 2019 kamar yadda Gwamna AbdulRazaq ya yi zargi," Lai ya faɗa.

A wani labarin kuma Yan Majalisa Sun Yi Fatali da Buƙatar Ɗage Dokar Hana Twitter

Majalisar wakilan tarayya ta yi watsi da buƙatar ɗage dokar gwamnatin tarayya ta hana amfani da twitter, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne yayin da take nazari kan rahoton kwamitocinta da suka gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: