Da Ɗuminsa: Bayan Komawarsa APC, Gwamna Matawalle Ya Sallami Dukkan Mashawartansa Na Musamman

Da Ɗuminsa: Bayan Komawarsa APC, Gwamna Matawalle Ya Sallami Dukkan Mashawartansa Na Musamman

  • Gwamna Matawalle na jihar Zamfara, ya sallami gaba ɗaya masu ba shi shawara na musamman banda mutum ɗaya
  • Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bayan ya sauya sheƙa zuwa APC a hukumance ranar Talata
  • Mai baiwa gwamna shawara kan tsaro, DIG Mamman Tsafe, shine kaɗai matakin korar bai shafe shi ba

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sallami dukkan mashawartansa na musamman (SA) banda mutum daya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da sakataren gwamnatin jihar na riƙo kuma shugaban ma'aikata, Alhaji Kabiru Balarabe, ya fitar.

KARANTA ANAN: Ba da Jimawa Ba Wasu Gwamnonin PDP Zasu Biyo Mu Zuwa APC, Gwamna Ya Faɗi Lokaci

Balarabe yace mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan tsaro, Mai ritaya DIG Mamman Tsafe, shine kaɗai wanda zai cigaba da riƙe muƙaminsa.

Wani ɓangaren jawabin yace:

"Muna sanar da al'ummar Zamfara cewa, Gwamna Bello Matawalle, ya sallami dukkan masu ba shi shawara ta musamman daga muƙamansu, amma banda mai bada shawara kan tsaro."

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
Da Ɗuminsa: Bayan Komawarsa APC, Gwamna Matawalle Ya Sallami Dukkan Mashawartansa Na Musamman Hoto: @bellomatawalle1
Asali: Instagram

Balarabe ya umarci dukkan waɗanda abun ya shafa da su miƙa al'amuran ofisoshinsu zuwa ga daraktocin dake ƙarƙashin su, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Hakanan kuma, Balarabe ya miƙa saƙon godiyar gwamna ga waɗanda wannan mataki ya shafa bisa gudummuwar da suka bada wajen cigaban jihar Zamfara

Gwamna Matawalle yayi haka ne saboda ya koma APC

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a ranar Talata 29 ga watan Yuni.

A cewar Balarabe, gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne saboda ya fice daga PDP ya koma APC.

KARANTA ANAN: Wata Sabuwa: Ministan Buhari Ya Ɓalle Daga Jam'iyyar APC, Ya Buɗe Sabuwar Sakateriya a Jiharsa

"Matakin sallamar masu bada shawarar na da alaƙa da sauya sheƙa zuwa APC, domin hakan zai bada damar zaƙulo wasu kwararru waɗanda za'a dama da su a gwamnatin, kuma ba tare da ɗuba banbanci ba." inji Balarabe.

A wani labarin kuma Ba Zamu Huta ba Har Sai Mun Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu, IGP

IGP Usman Baba, ya bayyana wa yan majalisar wakilai cewa hukumarsa na aiki ba dare ba rana domin bada tsaro ga yan Najeriya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Baba ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana gaban kwamitin kula da ayyukan hukumar yan sanda ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel