Najeriya Ta Hada Kai da Majalisar Dinkin Duniya Don Samarwa Kasa Abinci Mai Kyau

Najeriya Ta Hada Kai da Majalisar Dinkin Duniya Don Samarwa Kasa Abinci Mai Kyau

  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na jagorantar wani shiri don samar da abinci mai gina jiki a Najeriya
  • A cewarsa shirin zai taimaka wajen tabbatar da an samu ingantaccen abinci musamman ga yara masu tasowa
  • Gwamnatin Najeriya na ci gaba da fafutuka don samar da wadataccen abinci mai gina jiki ga 'yan Najeriya

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo na jagorantar hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dinkin Duniya don inganta tsarin abinci a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na nufin magance yunwa, magance rashin abinci mai gina jiki, rage cututtukan da ke da alaka da abinci da sauransu.

Osinbajo, a cikin jawabin da ya gabatar a taron tattaunawa na hadin gwiwa a Abuja, ya ce kokarin samar da tsarin abinci mai dorewa ya yi daidai da tsarin gwamnatin Buhari na kawar da talauci a duk fadin Najeriya.

KARANTA WANNAN: Kabilar Ijaw Ta Gargadi Buhari Kan Tamkawa Tsagerun Neja Delta da Ya Yi

Gwamnatin Buhari Ta Nemi Tallafin Majalisar Dinkin Duniya Kan Wadatar Najeriya da Abinci
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Osinbajo ya ce tsarin abinci dole ne ya kasance wadatacce don “tasiri” ga samar da abinci mai gina jiki kuma dole ne a hada karfi da karfe don rage adadin rashin abinci mai gina jiki.

“Dole ne mu gane cewa bayyana mahimman matakai don inganta tsarin abinci da kuma, samar da wadataccen abinci zai tabbatar da cewa lafiyar yara ya inganta, sun habaka, tare da inganta lafiyar kwakwalwarsu da tunani don koyo.

CBN Ta Gano Mafita Kan Tsadar Masara, Za Ta Tallafawa 'Yan Kasa

Babban Bankin Najeriya (CBN), a jiya Litinin, 28 ga watan Yuni, ya ce ya amince da sakin masara kimanin tan dubu 50 ga manyan masu samar da ita 12, karkashin dabarun samar da masara ta SMR da shirin Anchor Borrowers (ABP), Vanguard ta ruwaito.

Wannan shawarar, a cewar bankin, ita ce tsakaitawa da sarrafa farashin masara a kasuwannin Najeriya tare da dakile ayyukan 'yan handama da nufin tara masarar saboda su haifar da karancin abinci.

Wadanda zasu ci gajiyar yunkurin sun hada da Premier Flour Mills, Crown-Olam, Grand Cereals, Animal Care, Amobyn da Hybrid Feeds.

KU KARANTA: Yawan ku Ba Zai Hana Mu Karbar Mulki a 2023 Ba, PDP Ta Caccaki Gwamnonin APC

CBN Ta Kawo Mafita, Za Ta Karya Farashin Shinkafa a Najeriya

A daya bangaren, a kokarinsu na samar da wadataccen abinci ga 'yan Najeriya tare da karya farashin shinkafa, Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya, sun fara batun kaddamar da sayar da tan miliyan tara na tallafin shinkafa ga masu sarrafata.

Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele yayin da yake kaddamar da shirin sayarwar da kuma fara noman rani a Kaduna ya ce, bankin a shirye yake ko yaushe don tallafawa harkar noma, The Nation ta ruwaito.

Ahmed Mohammed na CBN reshen jihar wanda ya wakilci gwamnan, ya ce shirin an shirya shi ne don sayar da shinkafar a kan farashi mai rahusa da nufin karya farashin don amfanin kowa a Najeriya da ma wasu kasashen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel