'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta

'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta

  • 'Yan bindiga sun tare motar wani mutum tare da matarsa, sun hallaka matar sun sace mijinta
  • An ruwaito cewa, matar na dauke da juna biyu, duk da haka suka sa bindiga suka harbe ta a kan titi
  • Sai dai, ba a harbe ko sace sauran mutanen da ke cikin motar ba, lamarin da ya sanya ayar tambaya

Wasu ‘yan bindiga, a ranar Asabar, sun harbe wata mata mai ciki har lahira tare da yin garkuwa da mijinta a karamar hukumar Offa da ke Jihar Kwara.

Marigayiyar, wacce wasu majiyoyi suka bayyana sunanta da Hawa, matar Lukman Ibrahim, wani dillalin wayar salula a Kasuwar Owode wanda aka fi sani da "LUKTECH".

Lamarin, ya faru ne a daren Asabar 'yan mintoci kadan kafin karfe 7 na yamma yayin da Lukman ke tuka surukinsa, matarsa ​​mai juna biyu da yaronsu zuwa gida a kan hanyar Ojoku, kusa da Hedikwatar 'yan sanda.

KU KARANTA: Barnar Boko Haram da Na 'Yan Bindiga Basu Kai Illar Shan Miyagun Kwayoyi Ba

'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta
Wasu mutane dauke da bindiga | Hoto: news18.com
Asali: UGC

An rahoto cewa matar ta mutu nan take bayan harbin da aka yi mata kuma tuni aka wuce da gawarta zuwa dakin ajiyar gawarwaki na Babban Asibitin Offa.

Da take karin haske game da lamarin, wata majiya ta kusa da dangi ta shaida wa Daily Trust cewa:

“Marigayiyar ta kasance tana sana’ar sayar da magunguna a Oshunte, a kan hanyar Ibrahim Taiwo dake Offa.
“Mijin da aka sace yana tuka ahalin ne zuwa gida lokacin da bai wuce mintuna biyu ba zuwa Hedikwatar 'Yan sanda da ke kan titin Ojoku, wasu ‘yan bindiga bakwai da ake zargin Fulani ne suka kai musu hari kuma suka harbe matar kafin su yi awon gabada mijin.”

Sai dai ba a bayyana a yanayin da ya ba da damar kisan matar ba yayin da aka bar surukin da yaron.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) na rundunar ta jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma kara da cewa:

“ Rundunar na aiki tukuru don ganin an ceto wanda aka sace din ”.

Tsohon shugaba Jonathan ya magantu kan abinda ke jawo aikata laifuka a Najeriya

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya koka kan karuwar aikata laifuka a kasar yana mai cewa galibinsu shan miyagun kwayoyi ne ke jawo su.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi tir da bayyanar kungiyoyin asiri a makarantun sakandare da firamare.

A cewarsa, wannan ba karamin abin takaici bane saboda ya kara tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta magantu kan yunkurin hana shigo da tukunyar gas Najeriya

Cikakken Bayani: Fusatattun 'yan PDP sun yi garkuwa da jami’an zabe a Jigawa

A wani labarin, Rahotanni da Legit.ng Hausa ke samu sun bayyana cewa, mambobin jam’iyyar PDP da ke fusace a yanzu haka suna rike da jami’an aikin zabe saboda rashin bayyana sakamakon zaben da ake ganin dan takarar jam’iyyar ya lashe a wani sashi a karamar hukumar Birnin Kudu.

Hukumar zaben jihar ta gudanar da zabukan kananan hukumomi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar a ranar Asabar, Premium Times ta ruwaito.

An tsare jami'an ne a rumfar zaben tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a yankin Chiyako da ke karamar hukumar Birnin Kudu.

Jami'in tattara sakamakon zabe a rumfar an rawaito cewa ya tsere ba tare da bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben ba duk da cewa an kirga kuri'un.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.