Bayan Kame Nnamdi Kanu, Sojin Sama Sun Yi Kaca-Kaca da Sansanin IPOB

Bayan Kame Nnamdi Kanu, Sojin Sama Sun Yi Kaca-Kaca da Sansanin IPOB

  • Daga jihar Delta, rahoto ya bayyana yadda rundunar sojoji ta fatattaki maboyar mambobin kungiyar IPOB
  • An ce sojojin sama sun jefa bama-bamai a sansanonin mambobin kungiyar ta IPOB bayan gano inda suke
  • Wannan ya faru ne kwanaki kadan bayan kame shugaban haramtacciyar kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Delta, Muhammed Ari, ya tabbatar da cewa wata tawagar jami’an tsaro karkashin jagorancin rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta jagoranci wani samame inda ta jefa wasu bama-bamai a wasu sansanonin 'yan kungiyar IPOB a jihar Delta.

Tun da farko, Ari ya ce ‘yan sanda sun yi amfani da jirage masu saukar ungulu a kwaryar babban birnin jihar a kusa da lllah don tarwatsa mambobin IPOB tare da aika musu da alama cewa rundunar tana kan aiki.

KARANTA WANNAN: Bayan Kame Nnamdi Kanu, Yarbawa Sun Gargadi Sunday Igboho Kan Fafutukar Ballewa

Bayan Kame Nnamdi Kanu, Sojin Sama Sun Yi Kace-Kace da Sansanin IPOB
Jaruman sojojin saman Najeriya | Hoto: punchyinfo.com
Asali: UGC

Jairidar Vangurad ta ruwaito Ari na cewa:

“Illah ita ce matattarar IPOB. Sun zo ne daga Onitsha ta jihar Anambara domin sake haduwa a Illah. Dole ne mu fada musu cewa ba a maraba da su a jihar.

"Jihar Delta za ta yi musu zafi. Da zarar mun gano su, zamu tabbatar mun fatattakesu kuma idan ba a kula ba, mu yi maganinsu kamar yadda suke so.”

Babu wani hari da ya faru a yankin

Amma mukaddashin jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda, DSP Bright Edafe, ya bayyana tashin hankalin da ke yankin a matsayin karya, Leadership ta ruwaito.

Edafe ya ce mutane suna yada jita-jita ne kawai, yana mai cewa babu wani abu mai kama da hari a cikin al'umma.

Edafe ya ce:

“Babu wani abu makamancin haka a Okpanam, yankin yana cikin kwanciyar hankali. Idan suka ji karar harbe-harbe, sukan fara tunanin abinda ba ya faruwa. Zan iya gaya muku cewa abin da ke faruwa a Okpanam lamari ne na halin da ba zan tattauna a bainar jama'a ba."

Mazauna babban birnin jihar, Asaba, da garuruwan da ke makwabtaka da shi har da Okpanam sun kara kaimi wajen lura da yanayin tsaro.

Wannan ya biyo bayan da wata wasika a watan da ya gabata ta yi barazanar kai wa Asaba da Agbor hari idan har gwamna Ifeanyi Okowa bai janye goyon bayansa ga dokar hana kiwo a fili ba a yankin kudancin Najeriya.

Jefa bam din ya haifar da tashin hankali a Asaba, babban birnin jihar Delta musamman bangarorin lllah, karamar hukumar Oshimili ta Arewa yayin da hadaddiyar tawaga ta 'yan sanda da sojoji suka yi amfani da jirage masu saukar ungulu domin kai farmaki yankin.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Yadda Nnamdi Kanu Ya Kashe Mutane Sama da 60

Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba

A wani labarin, Mambobin haramtacciyar kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) sun harbe wani mutum, mai suna Paschal Okeke, wanda ke kera “layar cin nasara” ga kungiyar saboda gazawar layarsa wajen karesu na tsawon shekaru, in ji ‘yan sanda a jihar Imo.

Wata sanarwa daga ‘yan sanda ta ce, kungiyar ta fusata da cewa layar, wanda ya kamata ta sa ba za a iya cin nasara a kansu ba kuma su tsere wa farmakin jami’an tsaro ba ta yi wani tasiri ba.

‘Yan sanda sun ce kisan ya biyo bayan samun nasarar 'yan sanda na kai samame a maboyar kungiyar da kuma ragargazar mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.