An sha ‘yar dirama yayinda matsayi Osinbajo da Gambari suka yi karo a bikin nadin Sarkin Kano

An sha ‘yar dirama yayinda matsayi Osinbajo da Gambari suka yi karo a bikin nadin Sarkin Kano

  • An sha ‘yar dirama yayinda matsayi Osinbajo da Gambari suka yi karo a bikin nadin Sarkin Kano
  • Osinbajo ya bayyana cewa ya halarci taron ne a madadin shugaban kasa inda shima Gambari ya gabatar da kansa a matsayin wakilin Buharin
  • A yau Asabar, 3 ga watan Yuli ne dai aka mikawa Sarki Aminu sandar mulki

Matsayin mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sun yi karo a wajen nadin sarautar Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano a ranar Asabar.

Ado Bayero, Sarkin Kano na 15 ya karbi sandar mulkinsa a yau Asabar, 3 ga watan Yuli.

Manyan mutane da masu ruwa da tsaki sun halarci bikin wanda aka gudanar cikin annashuwa.

An sha ‘yar dirama yayinda matsayi Osinbajo da Gambari suka yi karo a bikin nadin Sarkin Kano
Gambari da Osinbajo Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: An shiga rudani yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki Zakzaky a Kaduna

An yi wani dan dirama lokacin da Jagoran bikin ya gayyaci Gambari, wanda shi ma kawu ne ga Sarki, don isar da sako na fatan alheri.

Gambari, wanda ya jagoranci tawagar zuwa wajen taron, ya sanar da taron jama’a cewa ya na karanta sakon ne a madadin Shugaban kasa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Jawabin nasa ya sabawa sanarwar da jagoran shirin ya bayar a baya, wanda ya ambaci Osinbajo a matsayin wakilin shugaban kasa.

A cikin sakon da Gambari ya karanta, ya ambato Buhari yana yabon kyawawan halaye na marigayi Sarkin Kano kuma mahaifin Sarkin na yanzu, wanda ya bayyana a matsayin mutum mai kyawawan halaye da ka'idoji.

"Na tuna tare da kewa, irin kwazo da jajircewa da yake nunawa koyaushe don tattabbatar duk wani abu da ya aminta da shi, halayyar da ta kusan kai shi ga rasa rayuwarsa a ranar 19 ga Janairun 2013 saboda tsayuwarsa ta yaki da 'yan ta'addan Boko Haram," in ji shi. .

Lokacin da jawabi ya iso kan Osinbajo, shima yace yana wakiltar shugaban kasar ne.

KU KARANTA KUMA: Dankari: Dalibi ya kwaikwayi shugaban ‘yan bindiga, ya bukaci Shugabar makaranta ta biya miliyan uku a Zamfara

Da yake magana cikin harshen Hausa a taron, mataimakin Shugaban kasar ya sake nanata sanannen maganar mutanen Kano cewa “Kano ko da mai ka zo, an fi ka.”

"Dukkanmu muna alfahari da wannan birni, muna alfahari da gadonsa na juriya da son mutanekuma cewa ya kasance gida ga dukkan 'yan Najeriya," in ji shi.

Yadda Kano ta cika ta batse da manyan mutane yayin da ake bikin bai wa Sarkin Kano sandar mulki

Da farko mun kawo cewa gwamnoni, Ministoci, Sanatoci, mambobin majalisar wakilai na daga cikin manyan mutanen da suka isa jihar Kano a yanzu haka domin biki nadin sarautar, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shima yana garin domin taron, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Za a yi bikin mika sandar mulki ne ga Alhaji Aminu wanda ya kasance Sarkin Fulani na 15 na masarautar Kano a yau Asabar, 3 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel