Hotunan yadda Kano ta cika ta batse da manyan mutane yayin da ake bikin bai wa Sarkin Kano sandar mulki

Hotunan yadda Kano ta cika ta batse da manyan mutane yayin da ake bikin bai wa Sarkin Kano sandar mulki

  • An nada Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15 a watan Maris na shekarar 2020 bayan Muhammad Sanusi II ya sauka daga karagar mulki
  • Nadin nasa, wanda aka shirya a ranar Asabar, 3 ga watan Yuli, ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibnbajo da sauran manyan ‘yan Najeriya
  • Sauran shagulgula da aka tsara domin nadin sarauta sun hada da hawan doki sannan Sarki zai gaishe da talakawansa

Gwamnoni, Ministoci, Sanatoci, mambobin majalisar wakilai na daga cikin manyan mutanen da suka isa jihar Kano a yanzu haka domin biki nadin sarautar, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shima yana garin domin taron, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Za a yi bikin mika sandar mulki ne ga Alhaji Aminu wanda ya kasance Sarkin Fulani na 15 na masarautar Kano a yau Asabar, 3 ga watan Yuli.

Kano ta cika ta batse yayin da ake bikin bai Wa Sarkin Kano sandar mulki
Tuni manyan mutane suka yi wa garin Kano tsinke domin halartan bikin nadin Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: PDP na cikin matsala yayin da APC ke zawarcin gwamnan Bayelsa Diri

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa za a gudanar da kasaitaccen taron ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Birnin Kano.

Da farko dai jaridar ta ruwaito cewa fadar Sarkin Kano ta ce za a girke jami’an tsaro 4,000 da suka hada da DSS, sojoji, jami’an Civil Defense da sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da aminci da cikakken tsaro har a kammala bikin.

Da yake bayani, Dan-Dalan Kano, Abbas Dalhatu, ya kara da cewa an ware kujeru 3,000 ga manyan baki, da wasu kujeru 13,000 na sauran mahalarta kasaitaccen bikin.

Abunda zai wakana bayan nadin sarautar

Bayan kammala mika wa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayeor sandar mulki, za a gudanar da hawa na musamman, daga baya kuma Sarki zai zaga a cikin gari don gaisawa da jama’arsa.

Hotunan yadda Kano ta cika ta batse da manyan mutane yayin da ake bikin bai wa Sarkin Kano sandar mulki
Manyan mutane sun isa Kano don bikin bai wa Sarkin Kano sandar mulki Hoto: Kano Focus
Asali: Facebook

Ga hotunan taron da shafin Kano Focus ta wallafa a kasa:

Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa fasinjoji da dama ciki har da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun tsallake rijiya da baya a yayin da jirgin Max Air da ya tashi daga Kano zai tafi Abuja ya samu matsalar inji mintuna 10 bayan tashi daga filin jirgin Kano, MAKIA.

KU KARANTA KUMA: APC ta yanke hukuncin karshe kan Yari da Marafa, ta ce lallai Matawalle ne jagoranta a Zamfara

Daily Nigerian ta ruwaito cewa jirgin na Max Air mai lamba VM1645 wanda ya kamata ya tashi karfe 1.30 na rana amma aka yi jinkiri mintuna 30.

Daga baya jirgin ya tashi misalin karfe 2 na rana da fasinjoji cike maƙil. An gano cewa jirgin ya fara jigiga a iska kimanin mintuna 10 bayan tashinsa hakan yasa ya yi saukar gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel