Dankari: Dalibi ya kwaikwayi shugaban ‘yan bindiga, ya bukaci Shugabar makaranta ta biya miliyan uku a Zamfara

Dankari: Dalibi ya kwaikwayi shugaban ‘yan bindiga, ya bukaci Shugabar makaranta ta biya miliyan uku a Zamfara

  • Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Zamfara ta cafke Anka Bashir, dalibin SSS 1 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya saboda nuna kansa a matsayin shugaban ‘yan fashi
  • An rahoto cewa Bashir ya kira shugaban makarantar ya kuma yi mata barazana kan ta biya kudi naira miliyan 3 don kaucewa sace dalibanta
  • Husaini Rabiu, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, ya bayyana a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli, cewa an kama wanda ake zargin ne bisa ga bayanin da shugabar makarantar ta bayar

‘Yan sanda a jihar Zamfara sun kama wani dalibin makarantar Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Anka, Tukur Bashir wanda ke SS1 a kan ayyukan ‘yan fashi da makami.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Bashir ya bayyana kansa a matsayin shugaban yan fashi domin yaudarar shugabar kwalejin a kan kudi naira miliyan uku.

Dankari: Dalibi ya kwaikwayi shugaban ‘yan bindiga, ya bukaci Shugabar makaranta ta biya miliyan uku a Zamfara
Dalibin ya kwaikwayi shugaban ‘yan bindiga sannan ya bukaci Shugabar makaranta ta biya miliyan uku Hoto: Bello Matawalle.
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa wanda ake zargin ya kira shugabar makarantar a waya, inda ya fada mata cewa shi shugaban ‘yan fashin ne.

Jaridar Nigerian Tribune ta kuma bayyana cewa Bashir ya bukaci shugabar makarantar da ta biya N3m idan ba haka ba shi da ‘yan kungiyarsa za su zo makarantar su sace daliban.

Yadda muka kama wanda ake zargi Anka Bashir

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Husaini Rabiu, ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli, inda ya kara da cewa an cafke Bashir.

“A ranar 1 ga watan Yuli, 2021, shugabar Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Anka, ta kai rahoto ga DPO na reshen Anka cewa wani mutum da ba a san ko wanene ba ya kira ta ya nemi a ba shi kudi naira miliyan 3 ko kuma ya afka wa makarantar sannan ya kai hari kan daliban.
“Bayan samun wannan korafi, sai ‘yan sanda suka shiga aiki suka cafke wani Tukur Bashir a karamar hukumar Bakura ta jihar. A yayin bincike, an gano wanda ake zargin dalibin makarantar dan SS1 ne.”

A wani labari na daban, mun ji cewa rikici ya rincabe a yankin Ojota na jihar Legas yayin da masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa suka bijirewa umarnin 'yan sanda suka fara zanga-zanga.

Duk da 'yan sanda da sojoji sun mamaye wurin zanga-zangar a sa'o'in farko na yau Asabar, masu zanga-zangar daga bisani sun tsinkayi wurin, Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma jami'an tsaro dauke da bindigogi sun yi kokarin hana su zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel