An shiga rudani yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki Zakzaky a Kaduna

An shiga rudani yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki Zakzaky a Kaduna

  • 'Yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar mabiya mazhabar Shi'a a jihar Kaduna
  • An tattaro cewa 'yan shi'an da ke neman a saki Shugabansu Sheikh Zakzaky sun karkatar da akalar zanga-zangar tasu a lokacin da suka hango motocin 'yan sanda
  • Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan Kaduna bai yi martani kan lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi

An samu rudani a babban kasuwar da ke Kaduna a ranar Juma’a lokacin da jami’an tsaro suka yi harbi da yawa a kokarinsu na tarwatsa ’yan kungiyar Shi’a da ke zanga-zangar ci gaba da tsare shugabansu, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

'Yan sanda sun samu labarin zanga-zangar kuma nan da nan suka tattara kansu zuwa yankin Sheikh Gumi na Babbar Kasuwar Kaduna don dakatar da masu zanga-zangar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Sunday Igboho: Gwamnonin kudu maso yamma sun gudanar da taron gaggawa

An shiga rudani yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki Zakzaky a Kaduna
‘Yan sanda sun fatattaki masu zanga-zangar neman a saki Zakzaky a Kaduna Hoto: The Nation
Asali: UGC

An tattaro cewa lokacin da mambobin IMN din suka ga ‘yan sandan wadanda suka killace yankin da motocinsu, nan da nan sai suka fasa zanga-zangar a yankin.

Wata da abun ya faru a idonta, Halima Ibrahim, ta ce ta shiga kasuwa kenan lokacin da ta ji harbe-harbe.

“Nan da nan na buya lokacin da na ji harbe-harben kuma lamarin gaba daya ya haifar da rudani a cikin kasuwar. Daga baya, na sami karfin gwiwa na bar motata inda nake jiran jin abin da ya faru. An gaya min cewa 'yan sanda sun zo kasuwar ne don su dauki wasu membobin kungiyar IMN sai suka yi harbi don tsoratar da su.
"Wani kwastamana, Mohammed Yunusa, ya gaya min cewa a ranar Laraba, wasu 'yan sanda suna wucewa kasuwar a cikin motarsu a kan aikinsu na yau da kullun lokacin da mambobin IMN suka far musu, suka lalata motar kuma sai da mutanen da ke ciki suka gudu don tsira da rayukansu."

Sai dai kuma, wani dan kungiyar IMN, Abdullah Usman ya ce

“Galibi mu kan fito kowane mako biyu mu yi zanga-zanga domin tunatar da’ yan Najeriya cewa har yanzu ana tsare da shugabanmu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa tun daga 2015. Da alama ’yan sanda sun samu wani rahoton sirri cewa za mu fito mu yi zanga-zanga saboda sun doke mu.
“Lokacin da muka ga an tura ‘yan sanda yankin da za a yi zanga-zangar, sai muka yanke shawarar dakatar da zanga-zangar kuma ina ganin don su ba mu tsoro, sai wasu ‘yan sanda suka shiga cikin kasuwar suka yi ta harbi a sama.
"Daga nan muka koma mararrabar Dan Mani da ke kan hanyar Nnamdi Azikiwe, don ci gaba da zanga-zangarmu, amma kuma an tura 'yan sanda wurin kuma a karshen mun soke dukkan zanga-zangar don gudun zubar da jini."

KU KARANTA KUMA: Dankari: Dalibi ya kwaikwayi shugaban ‘yan bindiga, ya bukaci Shugabar makaranta ta biya miliyan uku a Zamfara

Lokacin da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda, ASP Muhammad Jalige ya ce zai tuntubi Jami’in’ Yan sanda na shiyya (DPO) da ke kula da yankin sannan ya yi martani.

Sai dai kuma jaridar ta ce har yanzu babu wani bayani.

Mun Shiga Ƙuncin Rayuwa Saboda Tsare Mahaifanmu, 'Ya'yan El-Zakzaky Sun Koka

A wani labarin, 'Yaƴan shugaban ƙungiyar shi'a (IMN), Sheikh Ibrahim El-zakzaky, sun koka kan yadda gwamnati ta tsare iyayen su fiye da kwana 2,000 a hannun jami'an tsaro.

A wata zantawa da ɗaya daga cikin ƴaƴan Zakzaky, Suhaila Ibrahim El-zakzaky, tayi da BBC ta bayyana cewa a halin yanzun ba su da wani buri da ya wuce suga iyayen su a tare da su.

Legit.ng hausa ya gano cewa a ranar Alhamis 3 ga watan Yuni, 2021, Zakzaky ya cika kwanaki 2,000 cif a tsare, bayan kama shi da jami'an tsaro suka yi a watan Disamba, 2015 a gidansa dake Zariya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel