Bana goyon bayan wani dan arewa ya shugabanci kasa a 2023 - Shettima

Bana goyon bayan wani dan arewa ya shugabanci kasa a 2023 - Shettima

  • Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce ba ya goyon bayan wani dan arewa da zai fito ya zama shugaban kasa a 2023
  • Shettima, wanda ke wakiltar yankin Borno ta tsakiya a majalisar dattijai, ya bayyana cewa za a sami daidaito da adalci idan shugaban kasa na gaba ya fito daga Kudancin Najeriya
  • Har yanzu jam’iyyun APC da PDP ba su bayyana yankin da za su ba tikitin takarar shugaban kasa ba

Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce yana goyon bayan Kudancin Najeriya ta samar da shugaban kasa na gaba bayan mulkin Muhammadu Buhari.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Shettima ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli, a yayin gabatar da wani littafi.

KU KARANTA KUMA: Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa

Bana goyon bayan wani dan arewa ya shugabanci kasa a 2023 - Shettima
Shettima ya nemi a mika mulki ga yankin kudancin Najeriya a 2023 Hoto: Yahya Bulama Kyari
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya ce bayan mulki ya zauna a arewa na tsawon shekaru takwas, zai zama adalci a juya shi zuwa kudu.

Ya ce:

“Na yarda da daidaito da adalci. Bayan da mulkin ya zauna a arewa na tsawon shekaru takwas, akwai bukatar mika shi zuwa kudu."

KU KARANTA KUMA: Matawalle: Na koma APC ne don a samu da zaman lafiya da tsaro a Zamfara

Shettima ya soki kira ga ballewa Shettima, wanda ke wakiltar Borno ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa abin da kasar ke bukata shi ne hadin kai a tsakanin bangarorinta daban-daban, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya yi fatali da batun neman ballewar da ke faruwa a wasu sassan kasar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce babu wani shiri da zai sanya Najeriya ta zama kasa mai jam’iyya daya tilo

A gefe uda, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce yawan masu sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da sauran jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ba zai iya mayar da Najeriya zuwa kasa mai jam’iyya daya ba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Yahaya wanda shine shugaban kwamitin daukaka kara na zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Anambra na jam’iyyar APC ya yi magana da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli a Abuja.

Ya yi watsi da tsoron da ‘yan adawa ke nunawa cewa jam’iyyar APC na ingiza kasar zuwa mai jam’iyya daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel