Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa

Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa

  • Kwanaki bayan sauya shekar Gwamna Bello Matawalle zuwa APC, jam’iyyar ta kasu zuwa gida biyu a hukumance
  • Wannan ya kasance ne yayin da wani rashin jituwa ya kunno kai a jam'iyyar inda bangaren Yari da na Matawalle ke rikici a yanzu
  • Tuni, jigo a APC kuma na hannun daman Matawalle yayi kira da a kori Yari da magoya bayansa

Wani jigon jam'iyyar All Progressive Congress, APC, a jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ya nuna bacin ransa game da matakin da tsohon gwamna Abdul'azeez Yari da Sanata Kabiru Marafa suka dauka kwanan nan game da shawarar kwamitin rikon jam'iyyar na kasa.

Shugabannin jam'iyyar na kasa a lokacin sauya shekar gwamna Bello Matawalle da sauran mambobin jam'iyyar sun rusa majalisar zartarwar APC a Zamfara tare da ayyana gwamnan a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Booth rasuwa

Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa
Shugaban rikon kwarya na APC tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar Hoto: APC Nigeria
Asali: Facebook

Ana zargin Yari da Marafa da raba APC a Zamfara

Tsohon Gwamna Yari da Sanata Marafa sun ki amincewa da rusa majalisar zartarwar APC a jihar, suna masu cewa wani yunkuri ne na mika jam'iyyar ga sansanin Gwamna Bello Matawalle.

Amma, Shinkafi a wani taron manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli, ya yi kira ga jam’iyyar ta kasa da ta yi maganin duk wanda ya karya dokar APC a Zamfara.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya nuna bakin cikinsa yayin da yake alhinin mutuwar dan majalisar Zamfara da wasu 'yan fashi suka kashe

Ya bayyana matakin Yari da magoya bayansa a matsayin wani yunkuri na haifar da wani bangare a cikin jam'iyyar yayin da ya yi kira ga shugabannin jam'iyyar APC na kasa da su kori Yari da Marafa.

Gidan talabijin Television Continental ya ruwaito cewa Shinkafi ya kuma yi kira ga gwamna Nasir El-rufai da ya nisanta da siyasar jihar Zamfara sannan ya guji yin rufa-rufa ga Yari da Marafa.

Kiran da Shinkafi ya yi ya nuna cewa a yanzu APC ta rabu gida biyu a hukumance.

Sanata Marafa ya mayar da martani, ya caccaki shugabancin APC na kasa

Da yake magana da gidan Talabijin na Arise a wannan ranar, Sanata Marafa ya bayyana cewa sauya shekar gwamnan kuskure ne a cikin doka.

Sanata Marafa ya kuma bayyana cewa kwamitin riko na Mai Mai Buni na jam'iyyar APC haramtacciyar kungiya ce.

Jagorancin APC a Zamfara: Yariman Bakura Ya Magantu Kan Cancantar Gwamna Matawalle

A wani labarin, mun ji cewa tun bayan da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya koma jam'iyyar APC, shugaban riko na jam'iyyar Maimala Buni ya sanar da nadin gwamna Matawalle a matsayin jagoran jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

Bayyana Matawalle a matsayin jagoran jam'iyyar APC ya jawo fushi ga wasu jiga-jigan 'yan siyasar jihar Zamfara, wadanda suka hada da, tsohon gwamna Abdulaziz Yari da tsohon dan majalisar dattawa Kabiru Marafa yayin da suka ki amincewa da nadin.

A nasa bangaren, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Yariman Bakura, ya bayyana amincewarsa da nadin, tare da bayyana dalilai daga tsarin mulkin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel