Matawalle: Na koma APC ne don a samu da zaman lafiya da tsaro a Zamfara

Matawalle: Na koma APC ne don a samu da zaman lafiya da tsaro a Zamfara

  • Komawaga APC za ta taimaka kwarai wajen gina Zamfara, in ji Matawalle
  • Matawalle ya ce karfin jam'iyya mai mulki zai bawa yan jihar damar shan romon demokradiyya
  • Gwamnan ya bukaci a hada hannu da yan adawa wajen dakile matsalar tsaro a jihar

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce yayi amannar cewa matsalar tsaron jihar tazo karshe tunda ya koma jam'iyyar APC, The Cable ta ruwaito.

Da yake jawabi a shirin Osasu ranar Juma'a, Matawalle ya shaida cewa komawa jam'iyya mai mulki, jihar zata kurbi romon demokradiyya.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan jiharZamfara, Bello Matawalle. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Gwamnan ya kuma kara da cewa ficewar sa daga PDP zuwa APC ba abu ne da ya saba ka'ida ba, yana mai cewa Zamfara za ta kara samun tagomashi sakamakon wannan mataki kamar yadda Pulse NG ta ruwaito

A cewarsa:

"Matsalar tsaro babu ruwan APC ko PDP. Ya kamata mu hada hannu waje guda don mu magance matsala."
"Siyasa ba abu ne kwarin gwiwa ko sha'awa ba. Yan siyasa da dama sun chanja jam'iyya, to don nayi ba sabon abu bane don nayi don samar wa da jihata zaman lafiya.
"Mun samu gagarumar nasara, musumman kan yan bindiga inda muka yi amfani da dabaru na yaki da na maslaha. Wasu daga cikin matakan kamar zaman sulhu, yayi aiki amma kasan ko a sulhun sai an shigar da siyasa.

KU KARANTA: Sojoji sun kama ɗan aiken ISWAP da aka tura Legas ya siyo wa 'yan ta'adda kaya

"Toh, ina so na tabbatar cewa a wa'adi na daya ya kare, zan hada kowa a jihar nan karkashin inuwa daya, muyi aiki tare, mu yi kokarin samar da ingantaccen tsaro ga jihar.
"Wannan ce jam'iyya mai mulki inda suke da sanatoci da yan majalisu. Muna da karfi kuma nasan mutate zasu fahimci dalili na. Inda da yake bani walaha yanzu cikin sauki zan same shi.
"Na yi amannar cewa wannan tafiya zan yi aiki tukuru tare da sauran gwamnoni yadda zamu samu kaso mai tsoka daga gwamnatin tarayya musumman kan rashin tsoro."

Dama tun kafin in chanja jam'iyya, nasan irin shirin da shugaban kasa ke yi na samar da karin kayan yaki don maganin wanda suka fitini arewacin Najeriya.

"Zamu samu karin jami'ai don korar yan bindigar, na tabbatar zaku ga chanje-chanje masu yawa, saboda zamu samu ci gaba a duk makaman da muke da su."

Ya kuma yi fatan cewa nan da wata uku, Zamfara zata fuskanci 'sauye-sauye da tarin yawa'.

'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

A wani labarin daban, Tajjudeen Yusuf, dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Kogi, ya ce Bello Matawalle gwamnan Zamfara dan siyasa ne da ke neman tazarce ido rufe, The Cable ta ruwaito.

Yusuf, dan majalisar tarayya na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan ne yayin martani game da sauya shekar Matawalle zuwa jam'iyyar APC a ranar Talata.

A wata sanarwa ranar Laraba, dan majalisar na Kogi ya zargi Matawalle da rashin aiki, ya kara da cewa gwamnan Zamfaran dan siyasa ne da ba jam'iyyar da za ta yi albahari da shi kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel