Gwamnan APC ya mayar da martani game da zargin da aka yi na kirkirar jam’iyya daya gabannin 2023

Gwamnan APC ya mayar da martani game da zargin da aka yi na kirkirar jam’iyya daya gabannin 2023

  • Gwamna Inuwa Yahaya ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa APC na kokarin mayar da Najeriya kasa mai jam'iyya daya
  • Gwamnan na Gombe ya ce sauye-sauyen shekar baya-bayan nan da APC ta ci galaba ba zai iya haifar da jam’iyya daya a kasar ba
  • Yahaya ya lura cewa hukumar zaben Najeriya, INEC, za ta ci gaba da yin rajistar sabbin jam’iyyu muddin suka cika ka’idoji

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce yawan masu sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da sauran jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ba zai iya mayar da Najeriya zuwa kasa mai jam’iyya daya ba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Yahaya wanda shine shugaban kwamitin daukaka kara na zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Anambra na jam’iyyar APC ya yi magana da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Shirin ciyar da dalibai: DSS ta kama malamai, jami'ai da masu sayar da abinci kan karkatar da kayayyaki

Gwamnan APC ya mayar da martani game da zargin da aka yi na kirkirar jam’iyya daya gabannin 2023
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce babu yadda za a yi Najeriya ta zama kasa mai jam'iyya dayaHoto: Muhammadu Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Ya yi watsi da tsoron da ‘yan adawa ke nunawa cewa jam’iyyar APC na ingiza kasar zuwa mai jam’iyya daya.

Maimakon haka, gwamnan na Gombe ya yi hasashen cewa za a samar da karin jam’iyyun siyasa don shiga cikin wadanda ake da su, matsawar sun cika bukatun INEC da tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Ya kuma yi iƙirarin cewa 'yan siyasa suna shiga APC ne saboda jam'iyya mai mulki ta fi nuna gaskiya ta fuskacin dangantakarta da dukkan mambobinta.

KU KARANTA KUMA: Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa

Kalmominsa:

“Jam’iyyar da ke kan mulki dole ne ta jawo hankalin mutanen da suke shirya don bayar da goyon bayansu kuma suna zuwa ne saboda sun fahimci cewa APC ta fi kafuwa, ta fi karfi da kuma gaskiya ta bangaren yadda take hulda da kowa ; na sama da na kasa."

Ba zan fita daga PDP ba - Gwamna Fintiri yayi watsi da maganar sauya sheka

A gefe guda, sakamakon jita-jita dake yaduwa a kafafen ra'ayi da sada zumunta cewa wasu sabbin gwamnonin PDP biyu na shirin komawa APC, gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa yayi martani.

The Nation ta ruwaito cewa Fintiri ya yi watsi da jita-jitan inda ya tabbatar da cewa ba zai fita daga PDP don shiga APC ba.

Gwamnan a jawabin da ya saki ta hannun Dirakta Janar na yada labaransa, Solomin Kumangar, ya ce babu kanshin gaskiya cikin maganar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel