Masu Garkuwa Sun Sace Shugaban Hukumar SRRBDA Na Sokoto a Gidansa Da Ke Katsina

Masu Garkuwa Sun Sace Shugaban Hukumar SRRBDA Na Sokoto a Gidansa Da Ke Katsina

  • Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun sace shugaban SRRBDA na Sokoto a gidansa da ke Katsina
  • Wasu daga cikin wadanda abin ya faru a idonsu sun ce yan bindigan kimanin su 10 ne suka shiga gidan suka fito da shi suka saka shi a mota
  • Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da afkuwar lamarin amma ta ce maharan su shida ne kuma akwai alama masu leken asiri suka basu bayani

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace shugaban hukumar kula da albarkatun ruwa ta Sokoto Rima River Basin Development Authority (SRRBDA), Labaran Muhammed Dandume, Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi masu nagarta a garin Dutsin-ma sun ce yan bindigan sun kutsa gidansa ne da ke rikunin gidajen mai'aikatan SRRBDA a Dutsin-Ma misalin karfe 11.47 na daren ranar Laraba.

Taswirar Jihar Sokoto
Taswirar Jihar Sokoto. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Daily Trust ta ruwaito cewa Wasu mazauna unguwar da abin ya faru a idonsu sun ce yan bindigan kimanin su 10 sun tilasta masa shiga motarsu sannan suka yi awon gaba da shi zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Majiyoyi sun tabbatar da lamarin

Daya daga cikin majiyoyin ya ce:

"Yan bindiga kimanin su 10 sun kai hari rukuncin gidajen ma'aikatan SRRBDA da ke karamar hukumar Dutsin-ma na jihar Katsina a jiya (Alhamis) inda suka sace shugaban SRRBDA, Labaran Mohammed Dandume."

KU KARANTA: El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya yi matuƙar murnar kama Nnamdi Kanu

Akwai yiwuwar masu leken asiri suka kai wa maharan rahoto, Yan Sanda

Da aka tuntube shi, Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da lamarin yana mai cewa maharan su shida ne sun kuma lalaba cikin gidan sun ci galaba kan mai gadin sannan suka tafi da Dandume.

Isah ya ce akwai yiwuwar akwai wasu yan leken asiri a unguwar da suka bai wa maharan bayannai game da wanda ake sace din duba da cewa a ranar Laraba ya dawo daga hutu.

Sojoji sun kama ɗan aiken ISWAP da aka tura Legas ya siyo wa 'yan ta'adda kaya

Hedkwatar tsaro ta sojojin Nigeria ta ce dakarun Operation AWATSE sun kama wani Ibrahim Musa da ake zargin dan kungiyar ta'addanci na ISWAP ne a yankin Sango Otta a jihar Ogun, The Cable ta ruwaito.

A yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan rundunar daga ranar 18 zuwa 30 ga watan Yuni, Bernard Onyeuko, mukadashin direktan watsa labarai na sojoji ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin sintiri a unguwa Majidun a jihar inda aka kama Musa.

A cewarsa, bayannan sirri ya nuna cewa an tura Musa zuwa Legas ne domin ya siyo wa kungiyar ta ISWAP wasu kayayyaki da suke amfani da su a Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel