El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya yi matuƙar murnar kama Nnamdi Kanu

El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya yi matuƙar murnar kama Nnamdi Kanu

  • Nasir El-Rufai ya ce ya yi murna matuka bayan da gwamnatin Nigeria ta kamo Nnamdi Kanu
  • Gwamnan na jihar Kaduna ya ce ya yi farin ciki ne da kamen saboda Kanu ya tsere bayan bashi beli kuma yana kiran kasarsa gidan Zoo
  • El-Rufai ya kuma bayyana cewa akwai banbanci tsakanin Nnamdi Kanu da Yan bindiga da Boko Haram

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana farin cikinsa game da kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), News Wire ta ruwaito.

Ministan shari'a kuma Attoni Janar na kasa, Abubakar Malami (SAN), a ranar Talata, ya sanar yayin taron manema labarai cewa an kama Kanu tun a ranar Lahadi.

Nasir El-Rufai
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Da ya ke tsokaci a kan kamen lokacin da aka yi hira da shi a BBC Pidgin a ranar Juma'a, El-Rufai ya ce ya yi murna da kama Kanu saboda ya tsere bayan bashi beli sannan yana kirar Nigeria 'Zoo' wato gidan namun daji.

KU KARANTA: Da Duminsa: Sunday Igboho ya yi 'mi'ara koma baya' kan yin gangamin Yarbawa a Legas

Gwamnan ya ce:

"Na yi farin ciki sosai (lokacin da aka kama Nnamdi Kanu) saboda, da farko ya tsere bayan bashi beli, ya saka wadanda suka tsaya masa cikin matsala.

"Na biyu, yana kallubalantar iko da hukumomin kasa mai zaman kanta kuma yana tada rikici; yana kiran kasarsa a matsayin Zoo.

"Ya kamata wannan ya zama darasi ga dukkan wadanda ke kallubalantar ikon da kasar Nigeria ke da shi, su yi takatsantsan."

Banbanci tsakanin IPOB da Boko Haram da Yan Bindiga

Da aka masa tambaya kan matakan da gwamnat ke dauka kan Boko Haram da yan bindiga, gwamnan ya ce ba daya suke ba domin Boko Haram ba kire suke yi a raba kasa ba.

Ya kara da cewa 'yan bindiga ba su da jagora ko shugaba guda daya kaar yadda IPOB ke da Nnamdi Kanu.

KU KARANTA: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

El-Rufai ya ce:

"Aa! Aa! Aa! Mutane na kwatanta abubuwan da ba daya suke ba."

"Nnamdu Kanu ne shugaban IPOB, kungiyar da aka haramta. An san shi, yana magana da mutane sosai kuma kowa ya san inda ya ke.

"Idan aka dauki Boko Haram a misali. Shekau ya kasance yana buya tsawon shekaru 10 kuma sojoji suna yakarsa.

"Ba wai kama Shekau yana zaune a wuri daya bane a Saudiyya, yana rubutu a twitter yana cewa a raba Nigeria ko yana cewa Boko Haram ta tafi ta kashe Helen ko Nasir El-Rufai.

"Nnamdi Kanu yana wuri daya ne yayin da Shekau yakin sonkoro ya ke yi. Har yanzu akwai yan bindiga amma gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel