Ba zan fita daga PDP ba - Gwamna Fintiri yayi watsi da maganar sauya sheka

Ba zan fita daga PDP ba - Gwamna Fintiri yayi watsi da maganar sauya sheka

  • Gwamna Ahmad Fintiri na jihar Adamawa ya yi watsi da rade-radin cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a ranar 29 ga Yuni, tayi rashin gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle
  • Fintiri ya ce zai cigaba da kasancewa a PDP duk da gayyatar da APC ke masa

Sakamakon jita-jita dake yaduwa a kafafen ra'ayi da sada zumunta cewa wasu sabbin gwamnonin PDP biyu na shirin komawa APC, gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa yayi martani.

The Nation ta ruwaito cewa Fintiri ya yi watsi da jita-jitan inda ya tabbatar da cewa ba zai fita daga PDP don shiga APC ba.

Gwamnan a jawabin da ya saki ta hannun Dirakta Janar na yada labaransa, Solomin Kumangar, ya ce babu kanshin gaskiya cikin maganar.

Fintiri, ya jaddada cewa zai cigaba da kasancewa a PDP kuma ba shi da niyyar fita zuwa wata jam'iyyar.

Kumangar yace:

Gwamnan bai da niyyar fita daga PDP. Yana nan hankalinsa kwance yana jagorantar jam'iyyar a jihar Adamawa domin jin dadin al'umma.
Abinda yafi muhimmanci yanzu shine a Najeriya gaba daya su hada kai wajen fuskantar kalubalen da kasar ke fama da shi.

Gwamna Fintiri yayi watsi da maganar sauya sheka
Ba zan fita daga PDP ba - Gwamna Fintiri yayi watsi da maganar sauya sheka Hoto: Gov Ahmadu Fintiri
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel