Shirin ciyar da dalibai: DSS ta kama malamai, jami'ai da masu sayar da abinci kan karkatar da kayayyaki

Shirin ciyar da dalibai: DSS ta kama malamai, jami'ai da masu sayar da abinci kan karkatar da kayayyaki

  • An kame wasu mutanen da ke kula da shirin ciyar da dalibai na gwamnatin tarayya
  • Wadanda ake zargin da suka hada da malamai, masu sayar da abinci da jami’an yanki sun shiga hannun jami’an DSS ne bisa zargin karkatar da danyen abinci
  • A cewar rahoton, an kama yawancin wadanda ake zargin ne daga wata makarantar firamare da ke Minna, jihar Neja

Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kame malamai da jami'an yanki da ke kula da shirin ciyar da daliban makarantu na gwamnatin tarayya bisa zargin yin zagon kasa ga shirin.

An kuma kama wasu masu sayar da abinci guda 10 da ake zargi da hada baki da malamai da kuma ma’aikatan yankin don sauya tsarin, jaridar Thisday ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kwastam ta kama damin kudaden waje boye a kunzugun jariri a Filin jirgin saman Kano

Shirin ciyar da dalibai: DSS ta kama malamai, jami'ai da masu sayar da abinci kan karkatar da kayayyaki
DSS ta damke malamai, jami'ai da masu sayar da abinci kan karkatar da kayayyaki Hoto: @SadiyaFarouqOfficial
Asali: Facebook

An gano cewa mafi yawan wadanda aka kaman sun fito ne daga makarantar firamare ta Central Primary School da ke Minna, jihar Neja, yayin da aka kuma kama wasu daga makarantun Katcha da ke karamar hukumar Katcha, da kuma Gwada a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

Baya ga karkatar da danyen abinci da aka tanada don dalibai a makarantun, an tattaro cewa ana zargin wadanda aka kama a Gwada da kiretai 30 na kwai da aka shirya don karin kumallon wasu daliban, wadanda ake zargin sun sayar wa masu sayar da abinci na garin.

Sakamakon haka, an tattaro cewa ana sanya yara hudu su raba kwai daya kacal yayin cin abincinsu.

Jami’ar da ke kula da shirin ciyar da daliban, Misis Amina Guar, lokacin da aka tuntube ta, ta tabbatar da labarin, inda ta ce an sanar da jami’an tsaro game da ci gaban.

Ta ce kungiyar ta samu nasarar gano kiretan kwai da wadanda abin ya shafa suka karkatar da su ga masu sayar da shayi a garin Gwada, inda ta kara da cewa: “Mun sami nasarar kwato kwayayen tare da mayar da su makarantar da abin ya shafa.
“Gaskiya ne cewa wasu daga cikin malamanmu a makarantar Firamare ta Central a halin yanzu suna tare da DSS, hasali ma wasunsu sun suma da suka isa wurin.

KU KARANTA KUMA: Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa

“Ba mu yarda da cin hanci da rashawa kowane iri ba; ba za mu yarda da ci da gumin yara da basu ji ba basu gani ba,” in ji Guar, tana mai kara da cewa tana sauri don garzayawa ofishin DSS domin sanin halin da ake ciki.

Kulli yaumin muna ciyar da yan makaranta milyan goma, Hajiya Sadiya

A wani labarin, Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta sanar da cewa ta samu nasarar ciyar da daliban makaranta milyan goma karkashin shirin ciyar da yan makaranta a fadin tarayya watau NHGSFP.

Ministar tallafi, kula da annoba da jin dadin jama'a, Hajya Sadiya Umar Farouq, ta sanar da hakan a Abuja a bikin kaddamar da shirin rabon kayayyakin girki a Abuja, rahoton Punch.

A cewar Minista Sadiya, gwamnatin tarayya ta dauki masu girki sama da 100,000 aiki don yiwa daliban abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng