Amaechi ya sanar da ranar fara aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano da zai laƙume $1.2bn

Amaechi ya sanar da ranar fara aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano da zai laƙume $1.2bn

  • Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce nan da sati biyu za a fara aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano
  • Amaechi ya ce aikin da aka amince da yin sa tun 2017 zai lashe makuden kudi har Dallar Amurka Biliyan 1.2
  • Minista sufurin ya ce gwamnatin tarayya ta ware kaso daya cikin uku na kudin aikin yayin da sauran bashi za a ciwo daga China

Rotimi Amaechi, ministan sufuri na Nigeria ya ce za a fara aikin shimfida layin dogo na Kaduna zuwa Kaduna da zai lashe Dalla Biliyan 1.2 nan da makonni biyu, The Cable ta ruwaito.

Amaechi ya bada wannan sanarwar ne yayin wata taron manema labarai da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya a ranar Juma'a a Abuja.

Rotimi Amaechi
Ministan Sufurin Nigeria, Rotimi Amaechi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

The Cable ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta amince da aikin na layin dogo daga Kaduna zuwa Kano ne a Janairun shekarar 2017.

FG za ta yi hadin gwiwa da China don gina masana'antar kera kayan aikin layin dogo

Amaechi ya ce gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin a kalla Naira biliyan 100 domin yin aikin.

Ya ce a yayin da ake jiran bashin daga gwamnatin kasar China, kashi daya cikin uku na kudin aikin zai fito daga kasafin kudin gwamnatin tarayya.

A yayin taron manema labaran, Amaechi ya ce gwamnatin tarayya ya bada Dallan Amurka miliyan 280 domin aikin kuma nan gaba za ta bada cikin Dalla miliyan 100.

Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da gwamnatin China domin gina kamfanin kera kayan aikin jirgin kasa a Kajola, jihar Ogun da za a rantsar wannan shekarar.

Amaechi na son a rika yankewa barayin kayan titin jirgi hukuncuin kisa

A game da batun masu satar kayan aikin layin dogon, ya ce hakan na iya saka jirgi ya kauce daga hanya tare da kashe fasinjoji kuma hakan zai saka kasa asarar kudade don maye gurbinsu.

Ministan ya bukaci a saka hukunci mai tsauri inda ya bada shawarar cewa a tuhumi duk wanda aka samu yana satar kayan titin jirgin da laifin kisa.

Amaechi ya kara da cewa tuni an tura wasu yan Nigeria 300 zuwa kasashen waje domin yin karatu a bangaren fasahar jirgin kasa a China da za a dauke su aiki a ma'aikatar da zarar sun dawo.

A wani labarin daban, Majalisar Dattijai da ta Wakilai a Nigeria, a ranar Alhamis sun amince da kudirin dokar 'Petroluem Industry Bill' (PIB) sannan sun amince da bawa yankunan da ake hako man fetur a wurinsu kashi 3 cikin 100 na kudin man fetur, Daily Trust ta ruwaito.

Majalisar ta amince da kudirin dokar ne bayan ta yi nazari kan rahoton kwamitin hadin gwiwa na majalisar wakilai ta dattijai na PIB.

Majalisar Dattawa ta amince a rika bawa yankunan da ake hako man fetur a wurinsu kashi 3 cikin 100 duk da cewa yan majalisar yankunan kudu maso kudu sun nemi a rika basu kashi 5 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel