Da Duminsa: Majalisa ta amince da dokar PIB da aka shafe shekaru 13 ana tafka mahawara a kanta

Da Duminsa: Majalisa ta amince da dokar PIB da aka shafe shekaru 13 ana tafka mahawara a kanta

  • Majalisun dattijai da na wakilan Nigeria sun amince da kudirin dokar man fetur na PIB wacce tun 2008 aka gabatar da ita a majalisar
  • Dokar za ta bada daman yi muhimman sauye-sauye a kamfanin man fetur na kasa NNPC da hukumar daidaita farashin man fetur PPPRA
  • Har wa yau, majalisun sun amince a rika bawa yankunan da ake hako man fetur kashi 3 cikin 100 na kudin man fetur din duk da yan yankin kashe 5 suke so

Majalisar Dattija da ta Wakilai a Nigeria, a ranar Alhamis sun amince da kudirin dokar 'Petroluem Industry Bill' (PIB) sannan sun amince da bawa yankunan da ake hako man fetur a wurinsu kashi 3 cikin 100 na kudin man fetur, Daily Trust ta ruwaito.

Majalisar ta amince da kudirin dokar ne bayan ta yi nazari kan rahoton kwamitin hadin gwiwa na majalisar wakilai ta dattijai na PIB.

Majalisar Dattawan Nigeria.
Zauren Majalisar Dattawan Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

Majalisar Dattawa ta amince a rika bawa yankunan da ake hako man fetur a wurinsu kashi 3 cikin 100 duk da cewa yan majalisar yankunan kudu maso kudu sun nemi a rika basu kashi 5 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kafin amincewa da kudirin, majalisar ta yi zaman sirri tare da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva da shugaban kamfanin man fetur na Nigeria, NNPC, Mele Kyari.

Shugaban majalisa Ahmad Lawan ya taya yan majalisar murna yana mai cewa majalisa zubi ta 9 ta ciro tuta bisa amincewa da wannan babban kudirin da yanzu ya zama doka.

Ya ce:

"An ci galaba a kan 'shedanun PIB' a wannan zauren majalisar. Mun amince da kudirin ta zama doka."

Kazalika, majalisar wakilai ta tarayya ta amince da kudirin na PIB, ya zama doka bayan karanto shi karo na uku a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Sojoji sun kama ɗan aiken ISWAP da aka tura Legas ya siyo wa 'yan ta'adda kaya

Shugaban kwamitin wucin gadi a kan PIB, Moohammed Tahir Mongunu ya gabatar da kudirin yana mai nema a amince da shi misalin karfe 1 na rana.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya jinjinawa yan majalisar bisa amincewa da kudirin yana mai cewa babban nasara ne ga majalisar.

Kudirin na PIB ya kasance a majalisar tarayya tun shekarar 2008 amma an gaza amincewa da shi saboda sarkakiya da ke cikinsa da mabanbantan ra'ayoyi.

PIB: Sabuwar dokar mai za ta ruguza aikin NNPC da PPPRA a Najeriya

Tun a baya, jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin PIB na shekarar 2020 a gaban ‘yan majalisar tarayya.

Rahoton ya bayyana cewa wannan kudiri zai bada damar kafa sabon kamfanin man Najeriya.

A dalilin haka kuma za a yi fatali da kamfanin man NNPC. Idan wannan kudiri ya samu karbuwa kuma har ya zama doka, gwamnati za ta soke hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan mai a Najeriya.

Wannan kudiri ya ba Ministocin kudi da na man fetur ikon ganin yadda za ayi gwanjon dukiyoyi da duk kadarorin NNPC ga sabon kamfanin da za su gaje su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel