Kwastam ta kama damin kudaden waje boye a kunzugun jariri a Filin jirgin saman Kano
- An kama wani da ake zargi da fasakwabri ne wanda ya yi kokarin wasa da hankalin jami'an Kwastam
- An kama wanda ake zargin da kudaden kasashen waje cikin kunzugun jariri a Filin jirgin saman Kano
- A cewar hukumar ta NCS, an mika kudaden ga babbban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC
Jami'an hukumar Kwastam ta Najeriya sun kama wani da ake zargi da shigo da wasu kudaden kasar waje boye a cikin kunzugun jariri.
Ta hanyar amfani da bayanan sirri, jami'an NCS sun cafke mai laifin a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, jihar Kano, jaridar The Guardian ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa
A cewar kwamandan yankin, Kwanturola Suleiman Umar, jami’an sun kwace $184,800 da Riyal 1,723,310 na kasar Saudiyya daga hannun mai fasa kwabrin a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni.
Umar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli, yayin ganawa da manema labarai inda aka mika kudin ga hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a jihar.
Da yake mayar da martani, Shugaban shiyya na EFCC a Kano, Faruk Dogon-Daji ya sha alwashin cewa hukumar za ta gudanar da cikakken bincike sosai a kan lamarin kuma za a gurfanar da wanda ake zargin tare da mika kudin ga Gwamnatin Tarayya, jaridar Vanguard ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya nuna bakin cikinsa yayin da yake alhinin mutuwar dan majalisar Zamfara da wasu 'yan fashi suka kashe
Ma'aikacin otel da ya tsinci damin daloli a dakin baƙi kuma ya mayar
A wani labarin, wani dan Najeriya, Obiefoh Sunday, wanda ke aikin goge-goge a otal din Lagos Continental, ya nuna gaskiya a aikinsa.
Maigidansa, Muhammad Ashraf, a shafinsa na LinkedIn ya rubuta game da yadda saurayin ya samo wasu daloli na Amurka a daya daga cikin dakunan da ya je tsabtacewa bayan bakon da ya sauka a ciki ya tafi.
Yana tsintar kudin, nan take sai mai aikin goge-gogen ya sanar da hukumar otal din halin da ake ciki kuma an hanzarta shigar da kudin cikin asusun kungiyar kudaden da aka rasa masu shi.
Asali: Legit.ng