Gwamnan Najeriya ya yi hasashen watan da za a yi gagarumin sauye-sauyen sheka a APC da PDP

Gwamnan Najeriya ya yi hasashen watan da za a yi gagarumin sauye-sauyen sheka a APC da PDP

  • Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya ce nan ba da jimawa ba APC za ta fuskanci irin wannan sauyin shekar da PDP ke fuskanta a halin yanzu
  • Gwamnan na kudu maso gabas a ranar Talata, 1 ga Yuli, ya bayyana cewa wannan zai faru ne a watan Disambar 2021
  • Wike ya ce sauya shekar da ake tsammani wani bangare ne na sake fasalin shirye-shiryen babban zaben na 2023

A ra’ayin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, sauya sheka wani bangare ne na siyasar Najeriya da tsarin zabe.

Hasali ma, Wike a ranar Talata, 1 ga watan Yuli, ya yi hasashen cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a watan Disamba, za ta rasa manyan mambobinta da dama kamar yadda Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta rasa gwamnoni da sanatoci zuwa mambobinta a halin yanzu, Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Tsoffin hotunan tsohon Shugaban kasa Obasanjo da ke nuna shi jakadan Najeriya ne na kwarai

Gwamnan Najeriya ya yi hasashen watan da za a yi gagarumin sauye-sauyen sheka a APC da PDP
Gwamna Wike ya ce babu abun da zai sa ya bar PDP Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Gwamnan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Kelvin Ebiri, ya lura cewa ‘yan siyasa a kasar na ta kaura zuwa wuraren da suka fifita burinsu a babban zaben 2023.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamna Wike yayi watsi da ikirarin cewa gwamnonin PDP suna sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ne saboda tsoratarwa da sauransu.

Ya yi jayayya:

“Mutane suna sauya sheka; da dama za su sauya sheka. Sauya sheka wani bangare ne na tsarin zaben mu. Yayin da kake sauya sheka, mutane na shigowa. Akwai wadanda suke fushi a can (a APC), za su zo (PDP). Ku da kuke fushi a nan (a PDP), za ku tafi. Wannan shine wasan."

Da yake misali da jiharsa, Wike ya kara da cewa:

“Idan da tsokana ne, idan kuma ta tsoratarwa ne, idan ta hanyar tilas ce, to jihar Ribas ba za ta kasance a PDP ba. Domin. Idan akwai wata jiha da aka ba ta tsoro, idan akwai wata jiha da jam’iyya mai mulki ta hukunta, to jihar Ribas ce.”

Matawalle: Rikakken Gwamnan PDP ya ce ko shi kadai ya rage a Najeriya, ba zai shiga APC ba

A wani labarin, mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya soki tsofaffin abokan aikinsa a jam’iyyar PDP, da su ka sauya-sheka, su ka bi tafiyar APC mai mulki.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Gwamna Nyesom Wike ya na cewa gwamnonin da su ke barin PDP, su na shiga jirgin APC, ba su san abin da ya kamata ba.

Nyesom Wike ya yi wannan magana ne bayan ya fara jin rahoton cewa mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle zai fice daga jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel