Allah yayi wa zukekiyar jarumar Kannywood, Khadija Mahmud, rasuwa

Allah yayi wa zukekiyar jarumar Kannywood, Khadija Mahmud, rasuwa

- A safiyar Alhamis 6 ga watan Mayu ne masana'antar Kannywood ta tashi da alhini tare da dimuwa

- Jaruma Khadija Mahmud 'yar asalin garin Jalingo na jihar Taraba ce ta amsa kiran mahaliccinta

- Jarumar ta rasu ne bayan kwashe shekara daya da tayi tana jinyar wani ciwo mai kone jinin jiki

Allah da girma yake! Allah ya tabbatar mana da cewa dukkan rai zai dandana mutuwa.

A safiyar Alhamis, 6 ga watan Mayun 2021 ne jaruma Khadija Mahmud ta masana'antar Kannywood ta amsa kiran mahaliccinta.

Jarumar ta rasu a garin Jalingo na jihar Taraba wurin karfe 6 na safe yayin da take hannun mahaifiyarta suna hanyar zuwa asibiti.

Cike da rudewa da alhini mahaifiyar Khadija ta sanar da Mujallar Fim cewa wani asibitin kudi suka fara mika ta amma sai aka tura su FMC Jalingo ganin halin da take ciki.

KU KARANTA: Bauchi: Sarki ya dakatar da Wakilin Birni saboda zarta shi walkiya yayin hawan sallah

Allah yayi wa zukekiyar jarumar Kannywood, Khadija Usman, rasuwa
Allah yayi wa zukekiyar jarumar Kannywood, Khadija Usman, rasuwa. Hoto daga Fimmagazine.com
Asali: UGC

Suna hanyar zuwa ne Allah ya karba rayuwar Khadija. Khadija ta rasu tana da shekaru 35 da haihuwa.

Jaruma Khadija ta kwashe tsawon shekara daya tana jinya. Ciwon kuwa yana kone jinin jiki ne domin ko leda nawa na jini aka saka mata zai kone.

Ta kan samu lafiya na wani lokaci amma sai ciwon ya dawo gadan-gadan.

Daga cikin fina-finan da jarumar ta fito sun hada da Rikicin Duniya, Uwar miji ko Kishiya da kuma Uwar Mijina.

Muna fatan Allah yayi wa Khadija Rahama, yasa ta huta mu kuma ya kyautata zuwa tamu.

KU KARANTA: Jarumi Lawan Ahmad ya zabgawa jaruma mai tasowa mugun mari a wurin shirya fim

A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ce "dukkan 'yan Najeriya" ne suke bukatarsa da ya nemi kujerar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa.

A yayin jawabi a ranar Juma'a yayin da ake yin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Bello ya ce zai bada ansa ga wannan bukatar nan babu dadewa.

Gwamnan yace 'yan Najeriya suna bukatar dan takara da zai hada kan kasar nan, kuma ya yadda yana da dukkan nagartar da ake bukata domin zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel