Ba Zamu Huta ba Har Sai Mun Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu, IGP

Ba Zamu Huta ba Har Sai Mun Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu, IGP

  • IGP Usman Baba, ya bayyana wa yan majalisar wakilai cewa hukumarsa na aiki ba dare ba rana domin bada tsaro ga yan Najeriya
  • Baba ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana gaban kwamitin kula da ayyukan hukumar yan sanda ranar Laraba
  • Sufetan ya yaba da irin matakin kulawa da majalisa ke baiwa hukumar yan sanda domin sauƙaƙa musu aiki

Sufeta janar na yan sanda, IGP Usman Baba, yace hukumarsa na aiki ba dare ba rana domin samar da tsaro a faɗin ƙasa, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Baba ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin kula da al'amuran yan sanda na majalisar wakilan tarayya ranar Laraba.

KARANTA ANAN: Mun San Inda Yan Bindiga Suka Ɓoye Ɗaliban Islamiyyar Tegina, Gwamnatin Neja

A cewar IGP Baba, hukumar yan sanda ƙarƙashin jagorancin shi zata tabbatar da yan Najeriya na bacci "Idanuwan su biyu a kulle."

IGP Usmsn Baba
Muna Aiki Baji-Ba-Gani Domin Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu a Rufe, IGP Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yace: "Mun zo nan da yammacin nan ne domin tattaunawa tare da shugaba da mambobinsa na kwamitin dake kula da ayyukan hukumar yan sanda a majalisar wakilai."

"Kuma domin mu tattauna a kan hanyoyin da zasu sauƙaƙa mana aikin mu, sannan mu fahimci juna saboda manufar mu guda ɗaya na kyautata ayyukan yan sanda ga yan Najeriya. Mu tabbatar suna kasuwancin su cikin kwanciyar hankali."

"Hakanan kuma muna aiki iyakacin kokarin mun wajen samar da kyakkyawan jagoranci ga jami'an yan sanda."

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Ƙasar Burtaniya Zata Taimakawa Nnamdi Kanu, Shugaban IPOB

IGP ya yaba da namijin ƙoƙarin yan majalisa

Sufetan yan sanda, Usman Baba, ya yaba da yanayin yadda yan majalisa suke nuna damuwarsu da kokarin inganta aikin ɗan sanda.

Yace: "Muna alfahari da abun da muka gani zuwa yanzun ta ɓangaren matakin kulawa da yan majalisa ta 9 da suke wa hukumar yan sanda domin sauƙaƙa mana aikin mu, sannan yan Najeriya su amfana da ingantaccen tsaro."

A wani labarin kuma Yan Majalisa Sun Bankaɗo Wata Sabuwar Badaƙala a Rundunar Sojin Ƙasa, Zasu Fara Bincike

Majalisar wakilai ta gano wata badaƙala a rundunar sojin ƙasa ta rashin biyan ƙananan sojoji alawus ɗinsu, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Majalisar ta umarci kwamitin ta dake kula al'amuran sojojim ƙasa ya gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel