Mun San Inda Yan Bindiga Suka Ɓoye Ɗaliban Islamiyyar Tegina, Gwamnatin Neja

Mun San Inda Yan Bindiga Suka Ɓoye Ɗaliban Islamiyyar Tegina, Gwamnatin Neja

  • Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ta san wurin da yan bindiga suka ɓoye ɗaliban da suka sace a Tegina
  • A cewar gwamnatin, a halin yanzu ta na tattaunawa ne da ɓarayin, amma ba zata biya kuɗin fansa ba
  • Ta yi kira ga iyayen yaran su kwantar da hankulansu, gwamnati a shirye take ta ɗauki mataki don kuɓutar da 'ya'yansu

Wata ɗaya bayan sace wasu ɗaliban makarantar islamiyyar Salihu Tanko dake Garin Tegin, jihar Neja, gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta san inda aka ɓoye su, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Ƙasar Burtaniya Zata Taimakawa Nnamdi Kanu, Shugaban IPOB

Gwamnatin tace a halin yanzun tana tattaunawa ne da yan bindigan, amma lokaci zai nuna idan za'a ɗauki wasu matakai masu tsauri domin kuɓutar da ɗaliban.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ahmed Matane, shine ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema Labarai a Minna.

Gwamnatin Jihar Neja
Mun San Inda Aka Ɓoye Ɗaliban Islamiyyar Tegina, Gwamnatin Neja Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewarsa, a yanzun gwamnati ba zata ɗauki matakin soji ba saboda ana cigaba da tattaunawa, kuma babu maganar biyan kuɗin fansa.

"Mun san inda ɓarayin suka ɓoye yaran, kawai muna ankare da yanayi ne, ba mu son cutar da yaran yayin da muka ɗauki matakin soji akan ɓarayin," inji shi.

Matane ya tabbatar da cewa gwamnati ka iya ɗaukar matakin soji matuƙar tattaunawar ba ta haifar da ɗa mai ido ba.

Ya ƙara da cewa buƙatun mu a wurin tattaunawan sun haɗa da, yan bindigan su tuba su daina wannan mummunan ɗabi'a, sannan kuma su saki yaran ba tare da cutar da su ba.

KARANTA ANAN: Yan Majalisa Sun Bankaɗo Wata Sabuwar Badaƙala a Rundunar Sojin Ƙasa, Zasu Fara Bincike

Gwamnati ta tabbatar wa iyaye zata kuɓutar da ƴaƴansu

Matane ya tabbatar wa iyayen da abun ya shafa cewa gwamnati zata kuɓutar da 'ya'yansu cikin ƙoshin lafiya, amma ba zata amince da biyan kuɗin fansa ga wasu yan bindiga ba.

Yace: "Gwamnati ta na taya iyayen da wannan lamari ya shafa jimamin da suke ciki kuma mun fahimci cewa suna son a ɗauki matakin gaggawa."

"Gwamnati na sane da bukatar iyaye na kuɓutar da yaran su cikin ƙoshin lafiya yayin da lokaci ke ƙara shuɗewa, amma ba zamu amince da biyan kuɗin fansa ba."

A wani labarin kuma APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP

Jam'iyyar APC ta yi watsi da zargin cewa tana shirya maguɗin zaɓe a babban zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban PDP, Uce Secondus, shine ya zargi jam'iyya mai mulki da ƙoƙarin komawa kan mulki ko ta halin yaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel