Yan Majalisa Sun Bankaɗo Wata Sabuwar Badaƙala a Rundunar Sojin Ƙasa, Zasu Fara Bincike

Yan Majalisa Sun Bankaɗo Wata Sabuwar Badaƙala a Rundunar Sojin Ƙasa, Zasu Fara Bincike

  • Majalisar wakilai ta gano wata badaƙala a rundunar sojin ƙasa ta rashin biyan ƙananan sojoji alawus ɗinsu
  • Majalisar ta umarci kwamitin ta dake kula al'amuran sojojim ƙasa ya gudanar da bincike kan lamarin
  • Hon. Nalaraba yace duk da karin kuɗin alawus da rundunar ta samu amma babu wani canji wajen biyan sojoji alawus

Majalisar wakilai ta tarayya ta ɗora wa kwamitinta dake kula da sojojin ƙasa alhakin gudanar da bincike kan ayyukan rundunar soji.

Majalisar ta ɗau wannan matakin ne saboda zargin da ake wa rundunar na ƙin biyan kuɗin alawus ga jami'anta da suka kai biliyan N663bn, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP

Majalisar ta bada wannan umarnin ne ranar Laraba biyo bayan kudirin da ɗan majalisa, Abubakar Nalaraba, ya gabatar a gabanta.

Yan majalisar wakilai
Yan Majalisa Sun Bankaɗo Wata Sabuwar Badaƙala a Rundunar Sojin Ƙasa, Zasu Fara Bincike Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ɗan majalisar ya jawo hankalin majalisar kan rashin biyan wasu sojoji haƙƙokinsu, duk da ƙarin kuɗin kasafi da ake turawa rundunar a shekarar 2020 da 2021.

Duk da karin kuɗi amma walwalar sojoji bata canza ba

Hon. Nalaraba ya bayyana cewa duk da ƙara kuɗin alawus na rundunar soji da aka yi a kasafin kuɗi daga biliyan N283bn a shekarar 2020 zuwa biliyan N380bn a 2021, amma babu wani abu da ya canza a kula da walwalar jami'an soji.

KARANTA ANAN: Labari Cikin Hotuna: Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru

Yace: "Kuɗin alawus da ake turawa sojoji ya ƙaru daga biliyan N283bn a 2020 zuwa biliyan N380bn a 2021 amma babu wani abu da ya canza a kula da jami'an soji."

"Kuma an riƙe wa jami'an sojin alawus ɗinsu waɗanda suka gudanar da opertion na musamman, ɗaukar horo da sauran su."

A wani.labarin kuma Abun Mamaki, Wani Fursuna Ya Yi Digirin Digirgir a Fannin Sadarwa a Gidan Yari

Wani fursuna dake zaman gidan gyaran hali a jihar Anambra ya kammala karatun digirin digirgir, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Jude Onwuzulike, ya karɓi takardun shaidar kammala karatun digirinsa na biyu daga jami'ar NOUN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel