Jerin sunaye: Jihohin APC da na PDP bayan sauya shekar Matawalle

Jerin sunaye: Jihohin APC da na PDP bayan sauya shekar Matawalle

Bayan watannin da aka kwashe ana ta rade-radi tare da musanta lamarin, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya koma jam'iyyar APC a ranar Talata, 29 ga watan Yuni.

A halin yanzu kuma cikin kwanakin nan, gwamnoni uku APC ta farauta daga PDP kafin zuwan zaben 2023.

KU KARANTA: Majalisar Igbo ta duniya: Sace Nnamdi Kanu aka yi, an tozarta shi fiye da 'yan Boko Haram

Jerin sunaye: Jihohin APC da na PDP bayan sauya shekar Matawalle
Jerin sunaye: Jihohin APC da na PDP bayan sauya shekar Matawalle. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƙanin Nnamdi Kanu ya bayyana kasar da aka kama yayan shi a Afrika

Gwamnonin da suka koma jam'iyyar APc daga PDP a cikin kwanakin nan sun hada da:

1. Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi

2. Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River

3. Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Bayan kammala zabukan gwamnoni na Edo da Ondo a 2020, APC tana da jihohi 20 yayin da PDP ke da jihohi 15. Jiha daya ce kadai a Najeriya da APGA ke da ita.

Amma kuma sabon cigaban da aka samu na sauya sheka ya sauya lissafin saboda APC ta dinga samun karuwa.

Jihohin da APC ke mulki a yankin kudu maso yamma

1. Jihar Ondo - Gwamna Rotimi Akeredolu

2. Jihar Ogun - Gwamna Dapo Abiodun

3. Jihar Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu

4. Jihar Osun - Gwamna Gboyega Oyetola

5. Jihar Ekiti - Gwamna Kayode Fayemi

Jihohin APC a yankin kudu maso gabas

6. Jihar Ebonyi - Gwamna Dave Umahi

7. Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodinma

Jihohin da APC ke mulki a yankin kudu kudu

8. Jihar Cross River - Gwamna Ben Ayade

Jihohin da APC ke mulki a yankin arewa maso yamma

9. Jihar Jigawa - Gwamna Mohammed Badaru Abubakar

10. Jihar Kebbi - Gwamna Abubakar Atiku Bagudu

11. Jihar Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai

12. Jihar Kano - Gwamna Abdullahi Ganduje

13. Jihar Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari

14. Jihar Zamfara - Gwamna Bello Matawalle

Jihohin da APC ke mulki a yankin arewa maso gabas

15. Jihar Borno - Gwamna Babagana Zulum

16. Jihar Yobe - Gwamna Mai Mala Buni

17. Jihar Gombe state - Gwamna Inuwa Yahaya

Jihohin da APC ke mulka a yankin arewa ta tsakiya

18. Jihar Niger - Gwamna Abubakar Sani Bello

19. Jihar Plateau - Gwamna Simon Lalong

20. Jihar Kwara - Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq

21. Jihar Kogi - Gwamna Yahaya Bello

22. Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule

Jihohin da PDP ke muli a yankin kudu maso yamma

1. Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde

Jihohin da PDP ke mulki a yankin kudu maso gabas

2. Jihar Abia - Gwamna Okezie Ikpeazu

3. Jihar Enugu - Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi

Jihohin da PDP ke mulka a yankin kudu kudu

4. Jihar Akwa Ibom - Gwamna Udom Emmanuel

5. Jihar Bayelsa - Gwamna Duoye Diri

6. Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki

7. Jihar Delta - Gwamna Ifeanyi Okowa

8. Jihar Ribas - Gwamna Nyesom

Jihohin da PDP ke mulka a yankin arewa maso yamma

9. Jihar Sokoto - Gwamna Aminu Tambuwal

Jihohin da PDP ke mulka a yankin arewa maso yamma

10. Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

11. Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed

12. Jihar Taraba - Gwamna Darius Ishaku

Jihohin da PDP ke mulka a yankin arewa ta tsakiya

13. Jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom

Jihohin da PDP ke mulka APGA a yankin kudu maso gabas

1. Jihar Anambra - Gwamna Willie Obiano

A wani labari na daban, kafin zuwan ranar gangamin da Yarabawa zasu yi a jihar Legas na ranar 3 ga watan Yuli, mai rajin kare hakkin Yarabawa, Sunday Adeyemo ya tabbatar da cewa zasu yi gangamin cikin lumana da kwanciyar hankali saboda bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya da shugabannin siyasa.

Adeyemo wanda ake kira da Igboho ya sanar a sabon bidiyon da ya fitar cewa za a yi gangamin duk rintsi ko tsanani, Vanguard ta ruwaito.

Vanguard ta wallafa cewa, yayi dogaro da irin gangamin da suka yi a jihohin Ogun, Oyo, Ondo da Osun inda yace gangamin Legas zai kasance na lumana kamar yadda aka yi a sauran jihohin kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel