Da Ɗuminsa: Ƙanin Nnamdi Kanu ya bayyana kasar da aka kama yayan shi a Afrika

Da Ɗuminsa: Ƙanin Nnamdi Kanu ya bayyana kasar da aka kama yayan shi a Afrika

  • Dan uwan Nnamdi Kanu, Kingsley Kanu ya tabbatar da cewa a kasar Kenya aka kama dan uwansa
  • Kamar yadda yace, kamensa take manyan hakkokinsa ne wanda kasar Kenya da Najeriya suka yi
  • Kanu yayi Allah wadai kuma yayi kira ga Birtaniya da ta shiga lamarin tare da kwatar wa dan uwansa hakkinsa

Kingsley Kanu, dan uwan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB ya ce an kama dan uwansa a kasar Kenya.

Gwamnatin tarayya ta yi shiru kuma bata sanar da inda ta kama Kanu ba, lamarin da yasa ake ta cece-kuce, Daily Trust ta ruwaito.

Amma a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, Kingsley ya ce hukumomin kasar Kenya sun kama dan uwanshi har sai da hukumomin tsaro na Najeriya suka je suka taso keyarsa.

KU KARANTA: Sauya Sheka: PDP bata da hankali da take wa Matawalle barazana, Fani-Kayode

Da Ɗuminsa: Ƙanin Nnamdi Kanu ya bayyana kasar da aka kama yayan shi a Afrika
Da Ɗuminsa: Ƙanin Nnamdi Kanu ya bayyana kasar da aka kama yayan shi a Afrika
Asali: Original

KU KARANTA: Hisbah ta kama matasa a Kano kan zarginsu da ayyukan badala, Kwamanda

Daily Trust ta tantance ikirarinsa. "Dan uwana Nnamdi Kanu yana da hakkin bukatar kafa Biafra. Yana da himma, hatta majalisar dinkin duniya ta san da ita. Saboda 'yan Biafra na goyo bayan Nnamdi Kanu, a yanzu haka ana tsaka da take masa manyan hakkokinsa na rayuwa."

"Da uwana ya fuskanci matukar gallazawa da ukuba a kasar Kenya da Najeriya. Sun take masa kusan dukkan manyan hakkokinsa da duniya ta bashi. Yanayin da aka kawo shi kasar nan yana daya daga cikin manyan laifukan da aka yi. Daga Najeriya har kasar Kenya dole ne a tuhumesu. Ina bukatar a yi wa dan uwana adalci, Nnamdi Kanu."

"Babbar hukumar Birtaniya a Najeriya dole ne ta jaddada cewa a saki dan uwana. Dole ne a tabbatar da kariya tare da tsaronsa. Dole ne a mayar da Nnamdi Kanu gida Ingila inda matarsa da 'ya'yansa ke rayuwa.

"Dole ne sakataren ketare, Dominic Raab, ya fito kiri-kiri ya bayyanawa hukumomin Najeriya cewa Ingila ta yi Allah wadai da abinda Najeriya da Kenya tayi na take dokoki da hakkoki.

"Sakataren ketare Raab ya fito fili, ya sanar dasu cewa akwai hukunci ga wadanda suka yi irin kamen da suka yi. Dole ne gwamnatin Birtaniya ta tabbatar da cewa an yi wa Nnamdi Kanu adalci."

A wani labari na daban, an janyo hankalin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, zuwa wata kasa a Afrika ne bayan an dauka alkwarin bashi tallafin miliyoyin daloli, jaridar TheCable ta gano hakan.

Shugaban IPOB wanda ke fuskantar wasu tuhuma da suka hada da cin amanar kasa bayan gangamin son rabe kasar Najeriya, ya tsallake belinsa da aka bada a 2017 bayan gurfana da yayi a gaban kotu.

Majiyoyin tsaro sun sanar da TheCable cewa an fara shirin kama Kanu tare da dawowa da shi kasar Najeriya da dadewa, amma sai ranar 27 ga watan Yuni aka samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng