Gangamin Yarabawa a Legas: Igboho yace bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya

Gangamin Yarabawa a Legas: Igboho yace bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya

  • Shugaban masu gangamin assasa kasar Yarabawa, Sunday Igboho, ya ce bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya
  • Ya sanar da hakan ne yayin shirin gangamin jihar Legas kuma kwanaki kadan bayan damke Nnamdi Kanu da aka yi
  • Ya tabbatarwa gwamnatin tarayya cewa zasu yi gangami cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da tashin-tashina ba

Kafin zuwan ranar gangamin da Yarabawa zasu yi a jihar Legas na ranar 3 ga watan Yuli, mai rajin kare hakkin Yarabawa, Sunday Adeyemo ya tabbatar da cewa zasu yi gangamin cikin lumana da kwanciyar hankali saboda bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya da shugabannin siyasa.

Adeyemo wanda ake kira da Igboho ya sanar a sabon bidiyon da ya fitar cewa za a yi gangamin duk rintsi ko tsanani, Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Hisbah ta kama matasa a Kano kan zarginsu da ayyukan badala, Kwamanda

Gangamin Yarabawa a Legas: Igboho yace bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya
Gangamin Yarabawa a Legas: Igboho yace bashi da karfin yakar gwamnatin tarayya. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Labarin biloniya mai shekara 60 wanda ya tara sama da N380b kuma yake yawo a keke

Vanguard ta wallafa cewa, yayi dogaro da irin gangamin da suka yi a jihohin Ogun, Oyo, Ondo da Osun inda yace gangamin Legas zai kasance na lumana kamar yadda aka yi a sauran jihohin kudu maso yamma.

"Bani da karfin ikon yakar gwamnatin Najeriya. A takaice dai ba zan iya yakar shugaban karamar hukuma ba. Amma wannan yakin na Ubangiji ne. Ubangiji ne zai yakar mana kuma sai mun samu kasar Yarabawa kuma mun kubuta daga bauta," yace.

"Nawa zamu iya? Sunday Igboho ba mutum bane mai karfin iko. Akwai mutane masu karfin iko a wurare da yawa, sai dai idan zamu yaudari kanmu. Ba zan iya wannan ni kadai ba. Dole ne mu hada kawunanmu amma dole yanzu a samu shugaba. An zaba Musa ya samarwa Isra'ilawa 'yancinsu kafin sauran su goya masa baya."

A bangaren kiran da yake na ware kasar Yarabawa daga Najeriya da kuma inda suke samun kudi, ya ce, "wadanda ke kasashen ketare ne ke tattara kudi kuma muke amfani dasu wurin siyan ababen hawa da sauran ababen bukata."

A wani labari na daban, an janyo hankalin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, zuwa wata kasa a Afrika ne bayan an dauka alkwarin bashi tallafin miliyoyin daloli, jaridar TheCable ta gano hakan.

Shugaban IPOB wanda ke fuskantar wasu tuhuma da suka hada da cin amanar kasa bayan gangamin son rabe kasar Najeriya, ya tsallake belinsa da aka bada a 2017 bayan gurfana da yayi a gaban kotu.

Majiyoyin tsaro sun sanar da TheCable cewa an fara shirin kama Kanu tare da dawowa da shi kasar Najeriya da dadewa, amma sai ranar 27 ga watan Yuni aka samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: