Majalisar Igbo ta duniya: Sace Nnamdi Kanu aka yi, an tozarta shi fiye da 'yan Boko Haram

Majalisar Igbo ta duniya: Sace Nnamdi Kanu aka yi, an tozarta shi fiye da 'yan Boko Haram

  • Majalisar Ibo ta duniya ta bayyana rashin jin dadinta kan kama Nnamdi Kanu da aka yi
  • Mai magana da yawun kungiyar da shugabanta sun ce sace Kanu aka yi kuma dabanci Najeriya ta nuna
  • Kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta kiyaye hakkokin Kanu kuma Amurka ta shiga lamarin

Majalisar Ibo ta duniya ta nuna damuwarta kan kama shugaban IPOB da aka yi da sace shi tare da nuna dabanci kuma aka dawo da shi kasar Najeriya da hanyar da bata dace ba.

Kungiyar a wata takarda da ta fitar a ranar Laraba ta ce an tozarta Kanu fiye da yadda ake wa 'yan ta'addan Boko Haram, kuma tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta baiwa hakkokinsa na dan kasa kariya, TheCable ta ruwaito.

A ranar Talata, Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce an kama Kanu, shugaban IPOB ta hanyar hadin guiwa da jami'an sirri na Najeriya.

KU KARANTA: Hisbah ta kama matasa a Kano kan zarginsu da ayyukan badala, Kwamanda

Majalisar Igbo ta duniya: Sace Nnamdi Kanu aka yi, an tozarci shi fiye da 'yan Boko Haram
Majalisar Igbo ta duniya: Sace Nnamdi Kanu aka yi, an tozarci shi fiye da 'yan Boko Haram. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Legas bayan Sunday Igboho ya sha alwashin gangami a jihar

"An dawo da shi Najeriya saboda ya cigaba da fukantar shari'ar da ya tsere ana yi bayan an bada belinsa kan laifuka 12 da ake zarginsa da su," Malami ya kara da cewa.

A wata takarda da Basil Onwukwe da Anthony Ejiofor, mai magana da yawun kungiyar da shugabanta, sun ce yadda aka dauko Kanu yafi kama da sace mutum tare da dabanci na tsakanin kasa da kasa wanda ya take dokar dauko mai laifi daga wata kasa.

"Duniya ta san da yadda ake yi wa 'yan ta'addan Boko Haram da makiyaya wadanda duniya ta san 'yan ta'adda ne," yace.

"Ana kama wadannan makasan, a sake su kuma daga baya a basu ayyuka a hukumomin tsaro. A daya bangaren, an saka ido kan Ibo inda aka bada umarnin a harbe su, kamawa da kuma sace su.

"Muna so mu jaddada cewa babu gwamnati a duniya ko wata hukumar tsaro ta duniya da suka tabbatar da cewa IPOB kungiyar 'yan ta'adda ce kuma babu inda a duniya aka taba nuna Nnamdi Kanu a matsayin dan ta'adda."

Kungiyar ta bukaci gwamnati da ta tabbatar da cewa an duba Kanu kamar yadda dokokin duniya suka bukata kuma a kiyaye masa hakkokinsa.

Ta kara kira ga gwamnatin Ingila da ta tashi tsaye domin kare hakkokin Kanu wanda yanzu dan kasarta ne, TheCable ta ruwaito.

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, ya zagi jam'iyyarsa kan barazanar da take na maka Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a gaban kotu kan sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC.

Fani-Kayode a jerin wallafar da ya dinga a shafinsa na Twitter, ya soki barazanar da ake wa Matawalle inda ya shawarci jam'iyyarsa da ta dage wurin janyo hankali, Daily Nigerian ta ruwaito.

"Barazanar da PDP ke yi na kai Bello Matawalle kotu a kan komawa jam'iyyar APC ta rashin hankali ce."

Asali: Legit.ng

Online view pixel