Da Ɗuminsa: Ƙasar Burtaniya Zata Taimakawa Nnamdi Kanu, Shugaban IPOB

Da Ɗuminsa: Ƙasar Burtaniya Zata Taimakawa Nnamdi Kanu, Shugaban IPOB

  • Gwamnatin ƙasar Burtaniya ta yi ikirarin baiwa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, wani taimako da ta kira da 'taimako na daban'
  • Shugaban sashin yaɗa labarai na ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya, Dean Hurlock, shine ya faɗi haka
  • Kanu na da takardar izinin zama a ƙasar Burtaniya da Najeriya, hakan yasa ya zama kamar ɗan ƙasar

Gwamnatin Burtaniya ta bayyana sha'awarta na samar da taimako bisa doka ga shugaban haramtacciyar ƙungiyar taware IPOB, Nnamdi Kadu, wanda FG ta sake kamawa ranar Lahadi, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Majalisa Sun Bankaɗo Wata Sabuwar Badaƙala a Rundunar Sojin Ƙasa, Zasu Fara Bincike

Shugaban sashin yaɗa labarai na ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya, Dean Hurlock, shine ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da Punch ranar Laraba a Abuja.

Nnamdi Kanu, Shugaban IPOB
Da Ɗuminsa: Ƙasar Burtaniya Zata Taimakawa Nnamdi Kanu, Shugaban IPOB Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake jawabi, Dean Hurlock, yace:

"Babban ofishin jakadancin Burtaniya dake Abuja ya fara bin matakai na neman ƙarin haske daga gwamnatin tarayya a kan yanayin cafke shugaban IPOB."

"Dangane da tambayar ko muna son taimakon shi ne, Muna tabbatar da cewa a shirye muke mu taimaka masa da 'taimako bisa doka"

Mr. Hurlock, ya ƙara da cewa gwamnatin Burtaniya na fatan FG zata gudanar da shari'ar Kanu ta hanyar bin matakan da ya dace da doka.

Da aka nemi yayi ƙarin haske kan me yake nufi da 'taimako a kan doka' Hurlock yace a duba wani kundin Burataniya "Taimakon Burtaniya ga yan ƙasarta dake waje'.

Wani sashi na kundin yace: "Zamu iya taimakonka da bayanai yayin da kake tsare, wanda ya ƙunshi taimako ta ɓangaren shirya maka ziyara, tura saƙo, damar yin aiki, da ayyukan jin daɗi da walwala."

"Amma ba zamu iya fitar da kai daga wurin da kake tsare ba, kuma ba zamu iya samar maka da abubuwa na musamman ba don kana ɗan Burtaniya."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Dalilin da Yasa Na Gudu, Nnamdi Kanu Yayi Jawabi a Gaban Kotu

Nnamdi Kanu yana da Fasfo ɗin Najeriya da Burtaniya

Kanu, wanda aka haifa ranar 25 ga watan Satumba 1967, yana da takardar shaidar zama a ƙasa Fasfo ta Najeriya da Burtaniya.

Bayan an kama shi, FG ta sake gurfanar da shi gaban Alkali Binta Nyako, ta babbar kotun tarayya dake Abuja ranar Talata.

Tun bayan wannan lokacin, Kanu na tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS.

A wani labarin kuma APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP

Jam'iyyar APC ta yi watsi da zargin cewa tana shirya maguɗin zaɓe a babban zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban PDP, Uce Secondus, shine ya zargi jam'iyya mai mulki da ƙoƙarin komawa kan mulki ko ta halin yaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel