Sauya Sheka: Rashin damokaradiyyar cikin gida ta sa gwamnoni ke tserewa, APC ga PDP

Sauya Sheka: Rashin damokaradiyyar cikin gida ta sa gwamnoni ke tserewa, APC ga PDP

  • Cece-kucen da ake yi kan cewa APC na kokarin juya akalar ko ina tare da mallaka kafin zuwan zaben 2023 ya samu suka daga APC
  • Kamar yadda sakataren jam'iyyar na rikon kwarya na kasa, John Akpanudoedehe yace, 'yan PDP na tserewa ne saboda babu adalci da damokaradiyya
  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya zargi APC da janye gwamnoni saboda su samu damar magudin zabe nan gaba

Abuja

A ranar Laraba da ta gabata, jam'iyyar APC tayi martani kan zargin da ake yi na cewa komen da wasu gwamnonin PDP ke yi zuwa APC hanya ce ta buga magudin zabe a 2023.

Premium Times ta ruwaito cewa a wata takarda da APC ta fitar ta hannun sakataren jam'iyyar na kasa, John Akpanudoedehe, ta ce 'yan jam'iyyar PDP na barin jam'iyyar ne tare da komawa APC saboda rashin adalci da suke fuskanta da kuma rashin damokaradiyyar cikin gida.

KU KARANTA: Hotunan iyalan Buhari da suka dira birnin London don yayen Hanan daga makaranta

Sauya Sheka: Rashin damokaradiyyar cikin gida ta sa gwamnoni ke tsere, APC ga PDP
Sauya Sheka: Rashin damokaradiyyar cikin gida ta sa gwamnoni ke tsere, APC ga PDP. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

KU KARANTA: Wurin kwadayi: Da tallafin maƙuden kudade aka yaudari Kanu har aka damke shi

Wannan martanin ya biyo bayan zargin da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus yayi bayan sauya shekar da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi zuwa APC.

Secondus ya zargi jam'iyya mai mulki da janye gwamnonin PDP saboda ta samu damar magudin zabuka masu gabatowa.

PDP ta caccaki APC kan farautar gwamnoninta da take

A ranar Talata, 29 ga watan Yuni, jam'iyyar PDP ta caccaki gwamnonin APC da gwamnatin tarayya kan farautar gwamnoninta da take ana tsaka da matsalar tsaro.

Kamar yadda jam'iyyar tace, a maimakon a mayar da hankali wurin shawo kan kalubalen tsaro a Najeriya, APC ta mayar da hankali wurin siyasa da janye gwamnonin PDP.

A wani labari na daban, majalisar Ibo ta duniya ta nuna damuwarta kan kama shugaban IPOB da aka yi da sace shi tare da nuna dabanci kuma aka dawo da shi kasar Najeriya da hanyar da bata dace ba.

Kungiyar a wata takarda da ta fitar a ranar Laraba ta ce an tozarta Kanu fiye da yadda ake wa 'yan ta'addan Boko Haram, kuma tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta baiwa hakkokinsa na dan kasa kariya, TheCable ta ruwaito.

A ranar Talata, Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce an kama Kanu, shugaban IPOB ta hanyar hadin guiwa da jami'an sirri na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel